Asara: Wani mutum mai shekaru 44 ya amsa laifin yi wa yar shekara 6 fyade

Asara: Wani mutum mai shekaru 44 ya amsa laifin yi wa yar shekara 6 fyade

Rundunar ‘yan sanda a jihar Ogun ta kama wani mutum mai suna Ragiu Moruf, dan shekara 44, bisa zargin sa da aikata fyade ga wata karamar yarinya mai shekaru 6 da aka boye sunan ta.

Kakakin rundunar ‘yan sanda a jihar Ogun, Abinbola Oyeyemi, ya ce ‘yan sanda sun kama mai laifin ne bayan Ranti Owonifaari, mahaifiyar yarinyar ta shigar da korafi a ofishin rundunar ‘yan sanda.

Mahaifiyar yarinyar ta ce wasu sabbin dabi’u da ta gani a wurin diyar ta ne ya kai ga ta gudanar da bincike a kan yarinyar.

Oyeyemi ta ce mahaifiyar ta sanar da rundunar ‘yan sanda cewar yarinyar da bakinta ta fadi yadda Rauf ya dauke ta zuwa dakinsa tare da yi mata fyade bayan mahaifiyar ta ga ruwan maniyyi a gaban yarinyar.

Asara: Wani mutum mai shekaru 44 ya amsa laifin yi wa yar shekara 6 fyade

Wani mutum mai shekaru 44 ya amsa laifin yi wa yar shekara 6 fyade
Source: Twitter

Kakain ta kara da cewar shugaban jami’an rundunar ‘yan sanda na Ofishin Idiroko, Amodu Aloko, ne ya jagoranci zuwa kama mai laifin.

DUBA WANNAN: Cin mutunci: An kama wasu garada uku da su ka zuba barkono a gaban wata budurwa

Aloko ya tabbatar wa da rundunar ‘yan sanda cewar wanda ake zargin ya amsa laifin sa, sannan an kai yarinyar asibiti domin gudanar da gwaje-gwaje.

Kazalika ya bayyana cewar kwamishinan ‘yan sandan jihar Ogun, Ahmed Iliyasu, ya bayar da umarnin gaggauta mayar da Rauf zuwa sashen binciken cin zarafin kananan yara da safarar mutane na rundunar ‘yan sanda domin daukan mataki nag aba a kan sa.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel