An ceto kananan yara 9 daga hannun masu safarar mutane a Katsina

An ceto kananan yara 9 daga hannun masu safarar mutane a Katsina

Hukumar kula da shige da fice na kasa wato Immigration ta ce jami'anta sun ceto kananan yara guda 10 daga hannun masu safarar mutane cikinsu har da jinjiri dan watanni tara da haihuwa.

Shugaban hukumar na jihar, Mr Ajisafe Olusola ne ya bayyana hakan cikin wata sanarwa da hukumar ta fitar ranar Laraba a Katsina kamar yadda Punch ta ruwaito.

Olusola ya ce yaran da aka ceto dukkansu ba su haura shekaru 11 da haihuwa ba inda ya kara da cewa an kama mutane biyu mata da ake zargi da hannu a safarar yaran masu suna Devorah Adewunmo mai shekaru 29 da Moriliya Ibrahim mai shekaru 31.

DUBA WANNAN: Yabon Buhari: Tsohon gwamnan jihar Bayelsa ya yiwa Jonathan gori

An ceto kananan yara 9 daga hannun masu safarar mutane a Katsina

An ceto kananan yara 9 daga hannun masu safarar mutane a Katsina
Source: Twitter

Shugbana na Immigration ya ce an damke mutane biyun da ake zargi ne a ranar 11 ga watan Fabrairu a jihar Katsina sakamakon bayanan sirri da hukumar ta samu a kansu.

Ya ce binciken da suka gudanar ya nuna cewa ana niyyar safarar yaran ne zuwa Libya inda za a bi da su ta Jamhuriyar Nijar ba tare da takardun tafiya na ainihi ba.

"Daya daga cikin wadanda ake zargin ta amsa cewa za su tafi wurin mijin ta ne da ke zaune a garin Agadez na Jamhuriyar Nijar inda zai taimaka musu zuwa Libya.

"Sun kuma yi ikirarin cewa sun rasa kudaden da za su ciyar da kansu da yaran ne da kuma kudin mota da za su tafi Agadez daga jihar Katsina," inji shi.

Olusola ya kara da cewa za a mika wadanda ake zargin da yaran ga Hukumar Hana Safarar Bil Adama na jihar Kano domin a cigaba da bincike a kan lamarin.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: : https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel