Kungiyoyin Duniya sun yi furuci kan zaben 2019 tsakanin Atiku da Buhari

Kungiyoyin Duniya sun yi furuci kan zaben 2019 tsakanin Atiku da Buhari

A yayin da ya rage sauran kwanaki uku kacal a gudanar da babban zaben kasa na kujerar shugaban kasa a ranar Asabar 16, ga watan Fabrairu, kungiyoyin duniya da dama gami da kafofin wata labarai sun tofa albarkacin bakunan su.

Da yawa da daga cikin masu nazari, masana ilimin da kuma sharhi akan harkokin siyasa na duniya, baya ga hasashe gami da kiyasi sun kuma bayyana ra'ayoyin su dangane da takara tsakanin shugaban kasa Muhammadu Buhari na jam'iyyar APC da kuma dan takara na jam'iyyar adawa ta PDP, Alhaji Atiku Abubakar.

Fitacciyar kungiyar nan ta duniya da ta shahara akan kiyasi da nazarin siyasa, Eurasia Group, ta bayyana cewa shugaban kasa Buhari zai ci galaba akan babban abokin adawar sa, dan takara na jam'iyyar PDP, Atiku.

Atiku da Buhari yayin rattaba hannu kan yarjejeniyar aminci da zaman lafiya gabani da kuma bayan zaben 2019

Atiku da Buhari yayin rattaba hannu kan yarjejeniyar aminci da zaman lafiya gabani da kuma bayan zaben 2019
Source: Facebook

Kungiyar Eurasia ta ce duk da mashahurancin da Atiku ya samu bayan nasarar sa a zaben fidda gwani na jam'iyyar sa ta PDP, hakan ba zai yi tasiri ba wajen samun nasara akan shugaba Buhari yayin zaben kasa da za a gudanar a ranar Asabar.

Cikin wani sharhi da kungiyar ta gudanar kuma ta wassafa ta hanyar kafofin watsa labarai a ranar 4 ga watan Janairun da ya gabata, ta bayyana cewa nasarar Buhari za ta tabbatar da shimfidar tsare-tsare musamman ta bangaren haraji da kuma ma'adanan man fetur.

Kazalika nasarar Atiku za ta dawo da martabar kasar nan na wani dan lokaci takaitacce gabanin Angulu ta koma gidan ta na tsamiya kamar yadda sharhin babbar kungiyar ta Eurasia ya bayyana.

Babbar mujallar nan da ta shahara akan fidda kididdiga da kiyasi akan tattalin arziki ta The Economist tare da kungiyar EIU Africa, sun yi hasashen cewa dan takarar kujerar shugaban kasa na jam'iyyar PDP, zai yi nasara a zaben kasar nan ta Najeriya.

KARANTA KUMA: Cikin Hotuna: Taron yakin zaben Buhari a garin Abuja

Cikin sharhin da mujallar Guardian ta duniya ta wassafa, ta ce gwamnatin shugaba Buhari ta gaza ta fuskar habaka tattalin arzikin kasar nan, tsanani na rashin tsaro da kuma kasawarta ta fuskar yakar cin hanci da rashawa da ta sha alwashi yayin yakin zaben ta na 2015.

A na ta ra'ayin, jaridar nan ta Financial Times ya kausasa harshe dangane da yadda gwamnatin shugaba Buhari ta sanya son zuciya da nuna bambanci yayin fafutikar ta wajen yakar rashawa da tsarkake Najeriya daga zangwanyewar tattalin arziki.

Sanarwa: Ku ci gaba da kasancewa tare da mu yayin da Shafin Naij.com Hausa ya sauya suna zuwa Legit.ng Hausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Domin shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.com

Ku biyo cikin shafukan mu na zaurukan sada zumunta:

https://facebook.com/legitnghausa

https://twitter.com/legitnghausa

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel