EU ta wassafa sunayen Saudiya, Najeriya da kasashe 21 masu kazamin Kudi

EU ta wassafa sunayen Saudiya, Najeriya da kasashe 21 masu kazamin Kudi

- Najeriya da Saudiyya sun shiga cikin jerin kasashen da ake yawo da kazamin kudi

- Kungiyar Tarayyar Turai ta sa Najeriya cikin kasashen da ke dar-dar da dukiyar ta

- EU ta shafawa wasu kasashen duniya 23 bakin fenti sakamakon rashin kyawawan tsare-tsaren ta fuskar tattalin arzikin su

Mun samu cewa, wasu kasashen duniya sun gamu da fushin kungiyar Tarayyar Turai sakamakon yadda ake samun yawaita da kai komo na kazamin kudi a sanadiyar rashin kyawawan tsare-tsare da ingantattun dokoki.

Kungiyar Tarayyar Turai ta jefa sunayen kasar Saudiya, Najeriya, Panama da kuma wasu kasashe da dama cikin jerin kasashen duniya ma su fuskantar barazana a sakamakon rikon sakainar kashi ta fuskar rashin kyawawan tsare-tsaren na batar da kudi wajen yakar ta'addanci.

Majiyar jaridar Legit.ng ta ruwaito cewa, kungiyar ta tarayyar Turai ta shafawa wannan kasashe baki fenti sakamakon yawaitar kai komo na kazamar dukiya cikin kasashen kamar yadda wani babban jami'in ta ya bayyana.

A yayin da ake ci gaba da gwagwarmaya ta sukar kungiyar EU sakamakon sanya kasar Saudiya cikin wannan jeranto, kungiyar tun a watan Janairun da ya gabata ta yanke shawarar hakan ba tare da sauraron kowane korafi ba kamar yadda kafar watsa labarai ta Rueters ta ruwaito.

KARANTA KUMA: Kungiyoyin Duniya sun yi furuci kan zaben 2019 tsakanin Atiku da Buhari

A halin yanzu akwai jerin kasashen duniya 23 da ke fuskantar fushin kungiyar EU inda a baya jeranton ya kunshi kasashe 16 kacal. Baya ga bata sunayen su, kasashen na ci gaba da fuskatar fushin kungiyar EU sakamakon mu'amalar harkokin kudi da ke tsakanin ta da su.

Jerin kasashen sun hadar da; Najeriya, Saudiya, Panama, Libya, Botswana, Ghana, Samoa, Bahamas, V*rgin Island, Puerto Rico, Guam, Samoa ta yankin Amurka, Afghanistan, Koriya ta Arewa, Habasha, Iran, Iraq, Pakistan, Sri Lanka, Syria, Trinidad and Tobago, Tunisa da Yemen.

Sanarwa: Ku ci gaba da kasancewa tare da mu yayin da Shafin Naij.com Hausa ya sauya suna zuwa Legit.ng Hausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Domin shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.com

Ku biyo cikin shafukan mu na zaurukan sada zumunta:

https://facebook.com/legitnghausa

https://twitter.com/legitnghausa

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel