Nasara ko fadu wa: Buhari ya roki Atiku ya karbi sakamakon zabe

Nasara ko fadu wa: Buhari ya roki Atiku ya karbi sakamakon zabe

- Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya roki yan takarar Shugaban kasa a zabe a mai zuwa da su bi hikimomin da ke tattare da shiga yarjejeniyar zaman lafiya domin ayi zabe cikin lumana

- Buhari ya roki Atiku da sauran yan takara da su karbi sakamakon zabe

- Atiku Abubakar ma ya fada ma Shugaban kasar da ya tabbatar da yayi amfani da matsayinsa wajen tabbatar da cewar duk wanda zai kada kuri’a azabe mai zuwa ya aminta da tsarin gudanarwar zaben

Shugaban kasa Muhammadu Buhari a ranar Laraba, 13 ga watan Fabrairu a Abuja ya roki yan takarar Shugaban kasa a zaben ranar Asabar, 16 ga watan Fabrairu da su bi hikimomin da ke tattare da shiga yarjejeniyar zaman lafiya domin ayi zabe cikin lumana.

Shugaba Buhari yayi wannan rokon ne a lokacin da shi da sauran yan takarar Shugaban kasa ciki harda tsohon mataimakin Shugaban kasa kuma dan takarar jam’iyyar Peoples Democratic Party (PDP), Alhaji Atiku Abubakar suka hadu a wajen sanya hannu a yarjejeniyar zaman lafiya.

Nasara ko fadu wa: Buhari ya roki Atiku ya karbi sakamakon zabe

Nasara ko fadu wa: Buhari ya roki Atiku ya karbi sakamakon zabe
Source: Facebook

Amma sai Atiku Abubakar ma ya fada ma Shugaban kasar da ya tabbatar da yayi amfani da matsayinsa wajen tabbatar da cewar duk wanda zai kada kuri’a azabe mai zuwa ya aminta da tsarin gudanarwar zaben.

KU KARANTA KUMA: Ka bari mutane su samu muradin ransu – Atiku ga Buhari

Da yake martani a wajen shiga yarjejeniyar, shugaba Buhari ya bayyana cewa abu mafi muhimmanci game da shirin shine don yan takara su amince da sakamakon zabe na karshe duk da cewar hukumar zabe mai zaman kanta ta rigada ta bayar da tabbacin cewa za ta yi komai don tabbatar da zabe na gaskiya.

Sanarwa: Ku ci gaba da kasancewa tare da mu yayin da Shafin Naij.com Hausa ya sauya suna zuwa Legit.ng Hausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Domin shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.com

Ku biyo cikin shafukan mu na zaurukan sada zumunta:

https://facebook.com/legitnghausa

https://twitter.com/legitnghausa

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel