Da dumin sa: ‘Yan Boko Haram sun bude wa tawagar Kashim Shettim wuta

Da dumin sa: ‘Yan Boko Haram sun bude wa tawagar Kashim Shettim wuta

Mayakan kungiyar Boko Harm sun bude wa tawagar gwamnan jihar Borno, Kashim Shettima, wuta, kamar yadda jaridar Sahara Reporters ta rawaito.

Gwamnan da tawagar sa na kan hanyar su ta zuwa Gamboru-Ngala daga Maiduguri, babban birnin jihar Borno, a lokacin da mayakan kungiyar su ka kai ma su harin.

Jaridar ta ce ‘yan Boko Haram din sun raba ayarin gwamnan biyu a yayin da su ke cikin tafiya tare da bude wuta ta kowanne bangare.

Gwamnan da tawagar sa za su ziyarci Gambro-Ngala ne domin gudanar da yakin neman zabe.

Sai dai jaridar Daily Trust ta bayyana cewar majiyarta ta shaida ma ta cewar mutane da dama sun rasa ran su, wasu kuma sun bata.

Da dumin sa: ‘Yan Boko Haram sun bude wa tawagar Kashim Shettim wuta

Tawagar Kashim Shettima
Source: UGC

Wani soja guda da wasu farar hula biyu sun mutu a kwanton baunar da mayakan su ka yi wa tawagar gwamnan, kamar yadda wata majiyar Legit.ng ta shaida ma ta.

DUBA WANNAN: 'Yan daba sun lalata motar yakin neman zaben APC a Kano

Mayakan sun kai wa tawagar harin ne a daidai garin Gajibo da ke karamar hukumar Dikwa.

Majiyar ta bayyana cewar harin bai ritsa da gwamna Shettima ba, saboda motar da ya ke ciki ta wuce kafin ‘yan ta’addar su bude wuta a kan ragowar ayarin da ke biye d gwamnan.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel