Atiku Abubakar ya bayyana muhimmin hakkin dake wuyan Buhari a 2019

Atiku Abubakar ya bayyana muhimmin hakkin dake wuyan Buhari a 2019

Dan takarar shugaban kasar Najeriya a inuwar jam’iyyar PDP, Alhaji Atiku Abubakar ya bayyana ma yan Najeriya wani muhimmin hakkinsu dake rataye akan wuyan shugaban kasa Muhammadu Buhari, inda yace wannan hakki shine tabbatar da sahihancin zaben 2019.

Legit.ng ta ruwaito Atiku ya bayyana haka ne yayin taron rattafa hannu akan yarjejeniyar zaman lafiya da kafatanin yan takarar shugabancin kasar Najeriya daga jam’iyyu daban daban suka halarta a babban birnin tarayya Abuja.

KU KARANTA: Mutane 3 sun sheka barzahu yayin arangama tsakanin Yansanda tsagerun IPOB a Imo

Atiku Abubakar ya bayyana muhimmin hakkin dake wuyan Buhari a 2019

Taron
Source: Facebook

A farkon jawabinsa, Atiku ya mika godiyarsa ga jam’iyyarsa ta PDP, da kuma kwamitin zaman lafiya a karkashin jagorancin tsohon shugaban kasa Janar Abdulsalami Abubakar da sauran mambobin kwamitin, inda yace sun nuna jajircewa da kuma kishin kasa wajen shirya wannan yajejeniya.

“Taruwarmu anan ya nuna muhimmancin wannan zabe a wajenmu, tare da nuna cigaban da aka samu a tafiyar dimukradiyyarmu, sai dai kafin na rattafa hannu akan yarjejeniyar, zan tuna maganan da tsohon shugaban kasa Jonathan ke yawan fada, inda yake cewa;

“Ban cancanci wani salwantar da rayuwarsa ko ya zubar da jini saboda takarata ba”, da wannan nake kira ga dukkanin jami’an hukumar INEC da jami’an Yansanda dasu tabbata sun tsare hakkin aikinsu ba tare da nuna bangarenci a zaben ba.

“Haka zalika ina kira ga hukumomin tsaronmu da kada su kuskura su fara farautar magoya bayan jam’iyyun hamayya kamar yadda aka saba yi a baya, fatanmu shine dimukradiyyarmu ta samu karin karfi bayan zaben 2019.” Inji Atiku.

Daga karshe Atiku yayi kira ga shugaba Buhari da ya tabbata duk wani dan Najeriya dake da ra’ayin kada zabe ya kada zabensa cikin kwanciyar, tare da tabbatar da kuri’ar tasa ta kirgu, sa’annan ya yi tuni ga abokan takararsa da cewa su saka Najeriya a gaba fiye da duk wani burace buracensu.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitcomhausa

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Source: Legit

Mailfire view pixel