Cikakken jawabin shugaban kasa yayin rattafa hannu kan yarjejeniyar zaman lafiya

Cikakken jawabin shugaban kasa yayin rattafa hannu kan yarjejeniyar zaman lafiya

Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya bayyana cewa hankulan yan Najeriya sun tashi musamman game da zaben ranar 16 ga watan Feburairu, na shugaban kasa, sai dai yace hakan ba wani sabon abu bane, yana faruwa a kowanne irin zabe ko gasa.

Legit.ng ta ruwaito Buhari ya bayyana haka ne yayin taron rattafa hannu akan yarjejniyar zaman lafiya da aka kulla tsakanin duka yan takarkarun shugabancin Najeriya a karkashin jagorancin shugaban kwamitin zaman lafiya ta kasa, tsohon shugaban kasa Abdulsalam Abubakar.

KU KARANTA: Masu garkuwa da mutane sun kashe wani babban Fasto, sun yi awon gaba da iyalansa a Zamfara

Cikakken jawabin shugaban kasa yayin rattafa hannu kan yarjejeniyar zaman lafiya

Taron
Source: Facebook

A jawabinsa, Buhari ya bayyana cewa zaben na 2019 na da matukar muhimmanci ga cigaban mulkin dimukradiyya a Najeriya, musamman duba da cewa shine zaben na farko da za’ayi bayan zaben 2015, wanda aka bayyanashi a matsayin mafi sahihanci a tarihin Najeriya.

“Haka zalika wannan zabe ya samo tagomashin shigar matasa da mata cikinsa ba kamar yadda aka saba a baya ba, hakan kuwa ya tabbata ne sakamakon samar da dokar baiwa matasa daman shiga a fafata dasu a siyasar kasar.

“Gashi kuma zaben zai fuskanci karin jam’iyyun siyasa da zasu fafata a cikinsa, zuwa yanzu muna da sama da jam’iyyun siyasa 70, wannan manuniyace ga kyakkyawar turbar dimukradiyyar da kasarmu ke kai. Don haka nake kira ga yan Najeriya su bada gudunmuwa wajen ciyar da dimukradiyya gaba.

“Haduwarmu anan munyi shi ne a gab da shiga zabe, kuma shine mataki na karshe a yakin neman zabe, zuwa yanzu dai yakin neman zaben ya kasance mai kyau, mun gode ma Allah, sai dai an samu wasu haddura da yayi sanadin mutuwar wasu jama’a, muna rokon Allah Ya jikansu, an gama kamfe saura kada kuri’a.” Inji Buhari.

Bugu da kari Buhari yace an shirya haduwar yan takarar shugaban kasar duka ne domin su dauki alkawarin bayar da gudunmuwa wajen ganin an gudanar da sahihin zabe, kuma su zamto masu daukan dangana da amincewa da sakamakon zaben.

“Don haka ina kira garemu damu cika wannan alkawari, domin zaunar da kasar cikin lafiya, dama hukumar INEC ta bamu tabbacin gudanar da zabe na kirki, hakan ne yasa na bata dukkanin abinda take bukata don shirya sahihin zabe, su kuma hukumomin tsaro mun tsawata musu akan daukan bangare a yayin zaben.” Inji shi.

A karshen jawabinsa, Buhari ya mika godiyarsa ga Patricia Scotland, babbar sakatariyar kasashen rainon Birtaniya, wanda ta samu halartar taron, sa’annan ya gode ma Abdulsalami Abubakar da sauran mambobin kwamitin zaman lafiya.

Daga karshe Buhari ya yi kira ga matasa dasu kauce ma fadawa hannun miyagun yan siyasa da zasu yi amfani dasu da miyagun hanyoyi domin samun biyan bukatarsu, sa’annan yayi kira ga jama’an Najeriya dasu sanya kasar cikin addu’o’insu don gudanar da zabe lafiya lau a tashi lafiya.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitcomhausa

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel