Ka bari mutane su samu muradin ransu – Atiku ga Buhari

Ka bari mutane su samu muradin ransu – Atiku ga Buhari

Tsohon mataimakin Shugaban kasa kuma dan takarar Shugaban kasa na jam’iyyar Peoples Democratic Party (PDP) a zaben ranar 16 ga watan Fabrairu, Alhaji Atiku Abubakar a ranar Laraba, 13 ga watan Fabrairu ya bukaci dan takarar Shugaban kasa a jam’iyyar All progressives Congress (APC), Shugaba Muhammadu Buhari, da ya tabbatar da cewa anyi zabe cikin lumana.

Ya kuma bukaci shugaba Buhari da ya kuma tabbatar da cewar hukumomin tsaro sun gudanar da ayyukansu yadda ya kamata.

Atiku ya bayyana hakan ne bayan sanya hannu akan yarjejeniyar zaman lafiya Abuja gabannin zaben Shugaban kasar wanda ya rage saura kwanaki uku kacal.

Ka bari mutane su samu muradin ransu – Atiku ga Buhari

Ka bari mutane su samu muradin ransu – Atiku ga Buhari
Source: Facebook

Dan takarar na PDP ya nemi Shugaban kasar da ya bari al’umman kasar su samu muradin ransu.

A baya legit.ng ta tattaro cewa Atiku Abubakar, yace kudirin takararsa bai cancanci zubar jinin kowani dan Najeriya ba.

KU KARANTA KUMA: Zabe zai kasance na gaskiya da amana – Buhari ya sake bayar da tabbaci

Abubakar wanda yayi Magana a wajen taron shiga sabuwar yarjejeniyar zaman lafiya a Abuja, ya ari furucin tsohon Shugaban kasa Goodluck Jonatan na 2015, inda ya jero muimmancin zabe na lumana da gaskiya.

Shugaban kasa Muhammadu Buhari a nasa martanin ya jadadda kira ga hukumar zabe mai zaman kanta akan zabe na gaskiya da amana.

Sanarwa: Ku ci gaba da kasancewa tare da mu yayin da Shafin Naij.com Hausa ya sauya suna zuwa Legit.ng Hausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Domin shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.com

Ku biyo cikin shafukan mu na zaurukan sada zumunta:

https://facebook.com/legitnghausa

https://twitter.com/legitnghausa

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel