Da duminsa: PDP ta maka INEC kotu kan dagewa akan lallai sai ta yi amfani da 'Card Reader'

Da duminsa: PDP ta maka INEC kotu kan dagewa akan lallai sai ta yi amfani da 'Card Reader'

- Jam'iyyar PDP ta maka hukumar INEC kotu akan dagewarta na lallai sai ta yi amfani da na'urar tantance masu kad'a kuri'a (Card Reader) a babban zaben kasar mai karatowa

- PDP ta bukaci kotun da ta dakatar da INEC daga dake duk wani zabe a rumfunan zabe idan har aka samu lalacewar na'urar tantance masu kada kuri'ar

- A baya INEC ta ce idan har aka samu lalacewar na'urori 'Card Reader', to za a soke zaben wannan rumfar zaben har sai an kawo wasu sabbin na'urorin

Jam'iyyar PDP ta maka hukumar zabe mai zaman kanta ta kasa INEC kotu akan dagewarta na lallai sai ta yi amfani da na'urar tantance masu kad'a kuri'a (Card Reader) a babban zaben kasar mai karatowa.

A cikin karar da PDP ta shigar gaban wata babbar kotun gwamnatin tarayya da ke Abuja, ta bukaci kotun da ta dakatar da INEC daga dake duk wani zabe a rumfunan zabe idan har aka samu lalacewar na'urar tantance masu kada kuri'ar.

A baya Legit.ng Hausa ta ruwaito maku cewa INEC ta ce idan har aka samu matsalar lalacewar na'urorin tantance masu kad'a kuri'ar, to za a soke zaben wannan rumfar zaben har sai an kawo wasu sabbin na'urorin, ko kuma dage zaben har sai washe gari idan har aka gaza musanya na'urarorin har zuwa karfe 2 na rana.

KARANTA WANNAN: Babbar magana: CUPP ta bankado wani shiri da ake yi na kashe kakakinta

Da duminsa: PDP ta maka INEC kotu kan dagewa akan lallai sai ta yi amfani da 'Card Reader'

Da duminsa: PDP ta maka INEC kotu kan dagewa akan lallai sai ta yi amfani da 'Card Reader'
Source: Facebook

A karar da PDP ta shigar mai dauke da kwanan wata, 11 ga watan Fabreru, jam'iyyar ta yi ikirarin cewa dagewar INEC na cewar lallai sai an tantance masu kad'a kuri'a da wannan na'urar ya saba da ka'idojin dokar zabe.

Sakin layi na 10 na abuwar dokar hukumar zaben ta bayyana cewa: "(a) La'akari da sashe na 49 (2) na dokar zabe, ya zama wajibi duk wanda zai kad'a kuri'arsa ya samu tantancewa daga wani mai kula kundin masu kad'a kuri'a ta hanyar amfani da na'urar tantance masu zabe (SCR), kamar yadda yake a cikin dokoki da tsare tsaren zaben.

"(b) Duk wani jami'in zaben da ya karya wannan dokar ta sakin layi na 10 (a) zai fuskanci hukunci na aikata laifi."

Jam'iyyar PDP ta ce wannan dokar da INEC ta sanya ya sabawa dokar zabe ta 49. Inda asalin dokar ta ce: "(1) Duk wani wanda ke son ya kad'a kuri'a da katin zabensa, zai gabatar da takardar zabe ga jami'in zabe (PO) a rumfar kada kuri'a da ke mazabarsa inda aka san sunansa na cikin kundin masu zabe."

Cikakken labarin yana zuwa...

SANARWA: Shafin jaridar NAIJ.com Hausa ya sauya suna zuwa Legit.ng Hausa. Muna fatan za ka ci gaba da kasancewa tare da Legit.ng Hausa don karanta labarai da dumi duminsu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukan mu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel