Jinin yan Najeriya bai cancanci zuba saboda takarata ba - Atiku

Jinin yan Najeriya bai cancanci zuba saboda takarata ba - Atiku

- Dan takarar shugaban kasa a jam'iyyar PDP Atiku Abubakar yayi kira ga masu shirin zubar da jini saboda shi

- Atiku yace kudirin takararsa bai cancanci zubar jinin kowani dan Najeriya ba

- Shugaban kasa Muhammadu Buhari a nasa martanin ya jadadda kira ga hukumar zabe mai zaman kanta akan zabe na gaskiya da amana

Dan takarar Shugaban kasa a jam’iyyar Peoples Democratic Party, Atiku Abubakar, yace kudirin takararsa bai cancanci zubar jinin kowani dan Najeriya ba.

Abubakar wanda yayi Magana a wajen taron shiga sabuwar yarjejeniyar zaman lafiya a Abuja, ya ari furucin tsohon Shugaban kasa Goodluck Jonatan na 2015, inda ya jero muimmancin zabe na lumana da gaskiya.

Jinin yan Najeriya bai cancanci zuba saboda takarata ba - Atiku

Jinin yan Najeriya bai cancanci zuba saboda takarata ba - Atiku
Source: Facebook

Shugaban kasa Muhammadu Buhari a nasa martanin ya jadadda kira ga hukumar zabe mai zaman kanta akan zabe na gaskiya da amana.

Shugaban kwamitin zaman lafiya, Janar Abdulsalami Abubakar (mai ritaya) ya kuma yi kira ga hukumomi tsaro dasu zamo tsaka-tsaki a lokacin zaben ranar 16 ga watan Fabrairu da kuma 2 ga watan Maris.

KU KARANTA KUMA: Yanzu-yanzu: Buhari, Atiku sun isa wajen rattaba hannu kan takardan lumana

A baya mun ji cewa Dan takarar Shugaban kasa a jam’iyyar Peoples Democratic Party (PDP), Alhaji Atiku Abubakar, a jiya Talata, 12 ga watan Fabrairu ya jadadda jajircewarsa na sauya fasalin lamuran kasar.

Atiku ya bayar da tabbacin cewa ba zai ba yan Najeriya kunya ba a alkawaran da ya daukar masu kamar ya jam’iyyar All Progressives Congress (APC) mai mulki tayi.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel