Babbar magana: CUPP ta bankado wani shiri da ake yi na kashe kakakinta

Babbar magana: CUPP ta bankado wani shiri da ake yi na kashe kakakinta

- Kungiyar hadakar jam'iyyun siyasa (CUPP), ta bayyana cewa ta bankado wani shiri da ake yi na kashe mai magana da yawun kungiyar na daya, Barr. Ikenga Ugochinyere

- CUPP ta zargi gwamnatin tarayya da kitsa wannan tuggun na kashe kakakin na ta

- Ta ce Mr Ugochinyere ya tsallake rijiya ta baya baya a wani hari da aka kaiwa rayuwarsa, da misalin karfe 8 na dare a kan hanyarsa ta komawa gida

Kungiyar hadakar jam'iyyun siyasa (CUPP), ta bayyana cewa ta bankado wani shiri da ake yi na kashe mai magana da yawun kungiyar na daya, Barr. Ikenga Ugochinyere.

Kungiyar CUPP a cikin wata sanarwa a safiyar ranar Laraba, daga hannun mai magana da yawunta na biyu, Mark Adebayo, ta zargi gwamnatin tarayya da kitsa wannan tuggun na kashe kakakin na ta.

"Da wannan muke sanar da daukacin 'yan Nigeria cewa a yanzu rayukan shuwagabannin jam'iyyun hamayya na cikin hatsari, wanda kuma ya ke hannun gwamnati, tilas ne a gareta ta kare rayukan jama'armu, idan har wani abu mummuna ya samu daya daga cikinmu, to kuwa gwamnatin ce zamu daurawa alhaki," cewar CUPP.

KARANTA WANNAN: Zaben 2019: Ba mu goyon bayan Atiku - Amurka ta mayarwa Keyamo martani

Babbar magana: CUPP ta bankado wani shiri da ake yi na kashe kakakinta

Babbar magana: CUPP ta bankado wani shiri da ake yi na kashe kakakinta
Source: Facebook

Sanarwar wacce CUPP ta rabawa manema labarai, Legit.ng ta samu daga jaridar Vanguard, ta yi ikirarin cewa Ugochinyere "ya tsallake rijiya ta baya baya a wani hari da aka kaiwa rayuwarsa, da misalin karfe 8 na dare a kan hanyarsa ta komawa gida daga wani taro da ya halarta."

Sanarwar ta labarta cewa bayan barin kakakin kungiyar, sai ya fahimci akwai motoci har guda biyu da ke bin bayansa, inda har ya kai kan gadar Mabushi. Bayan kara yin doguwar tafiya har zuwa kan titin filin jirgin sama, ya dan rage gudu domin tabbatar da ko motocin na binsa, a nan ne ya ga mutanen da ke cikin motar farko kirar Helux na dauke da bindigogi irin na jami'an DSS.

"Sun yi harbi har sau biyu amma cikin ikon Allah ba su samu Mr Ikenga ba. Motocin da ke wuce a wajen sun kara gudu jin karar harbin bindigar. Idan ba domin Allah ya kare ba, da sai dai aji labarin an kashe shi."

SANARWA: Shafin jaridar NAIJ.com Hausa ya sauya suna zuwa Legit.ng Hausa. Muna fatan za ka ci gaba da kasancewa tare da Legit.ng Hausa don karanta labarai da dumi duminsu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukan mu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel