Rayukan Mutane 14 sun salwanta yayin yakin zaben Buhari a jihar Ribas

Rayukan Mutane 14 sun salwanta yayin yakin zaben Buhari a jihar Ribas

Kimanin rayukan Mutane 14 ne suka salwanta a jiya Talata gabanin rufe taron yakin neman zaben dan takarar kujerar shugaban kasa na jam'iyyar APC, Muhammadu Buhari, da aka gudanar a babban birnin Fatakwal na jihar Ribas.

A jiya Talata shugaban kasa Muhammadu Buhari ya gudanar da taron sa na yakin neman zaben kujerar shugaban kasa cikin harabar filin wasanni na Amiesimaka da ke birnin Fatakwal na jihar Ribas.

Majiyar jaridar Legit.ng ta ruwaito cewa, rayukan Mutane 14 sun salwanta yayin taron yakin zaben shugaban kasa Buhari da aka gudanar a birnin na Fatakwal sakamakon turmutsetseniya da cinkoson al'umma da ta auku a mashiga ta harabar filin wasannin na Amiesimaka.

Buhari yayin taron yakin zaben sa a jihar Ribas

Buhari yayin taron yakin zaben sa a jihar Ribas
Source: Facebook

Tsautsayi da Hausawa kan ce ba ya wuce ranar sa kuma karar kwana ba ta tsallake kowane dan Adam, ta sanya rayukan al'umma suka salwanta a yayin yunkurin su na ficewa daga filin taron bayan shugaban kasa Buhari ya kammala yakin sa na zabe a jihar da ke Kudancin kasar nan.

Kazalika mutane kimanin takwas sun jikkata sakamakon yunkurin su na komawa bakin harkokin gaban su yayin da tururuwar al'umma ta yi tattaki akan su bayan halartar taron na yakin zaben shugaba Buhari.

Shafin jaridar The Punch ya ruwaito cewa, mummunan tsautsayin ya auku da misalin karfe 4.00 na Yammacin jiya Talata bayan da tuni shugaban kasa Buhari tare da 'yan tawagar sa ta jiga-jigan APC sun kama gaban su.

KARANTA KUMA: Buhari, Atiku za su kulla yarjejeniyar amincewa da yadda sakamakon zabe zai kasance

Kakakin hukumar 'yan sandan jihar Ribas, Nnamdi Omoni, ya tabbatar da aukuwar wannan mummunan tsautsayi da cewar a halin yanzu akwai kimanin mutane hudu da ke ci gaba da jinya a wani asibitin jihar.

Baya ga hukumar 'yan sanda, kakakin babban asibitin koyarwa na birnin Fatakwal, Kem Daniel-Elebiga, ya shaidawa manema labarai rahoto dangane da yadda aka killace gawarwakin mutane 14 da suka riga mu gidan gaskiya.

Sanarwa: Ku ci gaba da kasancewa tare da mu yayin da Shafin Naij.com Hausa ya sauya suna zuwa Legit.ng Hausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Domin shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.com

Ku biyo cikin shafukan mu na zaurukan sada zumunta:

https://facebook.com/legitnghausa

https://twitter.com/legitnghausa

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel