Zabe: Ba zamu saurara ba sai mun ga abinda ya ture wa buzu nadi a Ribas - Amaechi

Zabe: Ba zamu saurara ba sai mun ga abinda ya ture wa buzu nadi a Ribas - Amaechi

- Ministan sufuri, Rotimi Amaechi ya yiwa Gwamna Nyesome Wike na jihar Ribas kaca-kaca a kan butulcin da ya yi masa

- Mr Amaechi ya yi ikirarin cewa mutane da dama sun juya masa baya bayan ya kammala taimakonsu a rayuwa

- Tsohon gwamnan na jihar Ribas ya yi ya ce Gwamna Wike yana tsoron faduwa zabe shi yasa ya ke kokarin yin sulhu da APC

Ministan Sufuri Rotimi Amaechi ya lashi takobin fafatawa da Gwamna Nyesom Wike na jihar Ribas domin ganin jam'iyyar APC ta samu nasara a babban zaben kasa da ke tafe a ranar Asabar 16 ga watan Fabrairun 2019.

Ya yi wannan furucin ne yayin kaddamar da yakin neman zaben Shugaba Muhammadu Buhari da aka gudanar a jihar inda ya kara da cewa ba yau ne mutanen da ya amince da su suka fara cin cin amanarsa ba.

Ba yau aka fara yi min butulci ba: Amaechi ya ragargaji Gwamna Wike na jihar Ribas

Ba yau aka fara yi min butulci ba: Amaechi ya ragargaji Gwamna Wike na jihar Ribas
Source: Depositphotos

DUBA WANNAN: Asarar kujeru 50 a APC: Buhari ya bayyana rashin jin dadin sa

"A shekarar 2015, sojoji sunyi kokarin kama ni a yayin da na ke matsayin gwamna.

"Muna da gwamnan da ke ta kokarin yin sulhu da mu inda ya ke cewa zai bamu kuri'u a zaben shugaban kasa yayin da shi kuma yana son ya zarce a matsayin gwamna. Wannan ya nuna yana jin tsoro amma ba zamu fafata da shi har zuwa ranar zabe.

"Kashi 80 cikin 100 na wadanda suka zama manyan mutane a jihar Ribas sun ci albarkaci na.

"Wike ne shugaban ma'aikata na. Ni na nada shi shugaban majalisar zartarwa. Ni kuma na zabe shi a matsayin Minister amma daga baya da ya ga Goodluck Jonathan, sai ya juya min baya.

"Ba yau aka fara min irin wannan cin amanar ba har ma da sanatoci. Bayan ka gama taimaka musu, bayan ka musu addu'a za su juya maka baya saboda tukunyar abinci. Ranar Asabar ta mu ce."

Amaechi ya kara da cewa duk abinda PDP ta ke kullawa, APC a shirye ta ke domin tunkarar ta.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: : https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel