Wajibi ne mu binciki Obasanjo kan batan dala biliyan 16 - Buhari

Wajibi ne mu binciki Obasanjo kan batan dala biliyan 16 - Buhari

- Shugaba Buhari ya lashi takobin aiwatar da bincike kan dala biliyan 16, da gwamnatin Olusegun Obasanjo ta ce ta kashe wajen wadata kasar da hasken wutar lantarki

- Buhari ya ce gwamnatinsa za ta tabbatar da cewa an kwato biliyoyin dalolin da wasu suka yi sama da fadi a akansu, sannan kuma a hukunta su

- A halin yanzu Buhari yace dukkanin sakamakon zabe fara daga ranar Asabar 16 ga watan Fabrairu za su kasance na gaskiya da amana

Shugaban kasa Muhammadu Buhari, ya lashi takobin aiwatar da bincike kan dala biliyan 16, da gwamnatin tsohon Shugaban kasa, Olusegun Obasanjo ta ce ta kashe wajen wadata kasar da hasken wutar lantarki.

Buhari, wanda ya dauki wannan alkawari a ranar Talata, 12 ga watan Fabrairu yayin yakin neman zabensa a garin Yenagoa na jihar Bayelsa, ya ce gwamnatinsa za ta tabbatar da cewa an kwato biliyoyin dalolin da wasu suka yi sama da fadi a akansu, sannan kuma a hukunta su.

Wajibi ne mu binciki Obasanjo kan batan dala biliyan 16 - Buhari

Wajibi ne mu binciki Obasanjo kan batan dala biliyan 16 - Buhari
Source: Facebook

A tsakanin shekarar 1999 zuwa 2007 gwamnatin Obasanjo, ta bayyana kashe dala biliyan 16 kan inganta samar da hasken lantarki a Najeriya, sai dai har yanzu ana fuskantar kalubalen rashin wutar a sassan kasar.

KU KARANTA KUMA: Ba zan baku kunya ba kamar APC - Atiku

Jim kadan bayan alwashin na Buhari, sai manema labarai suka tuntubi kakakin tsohon shugaba Obasanjo dangane da lamarin, Kehinde Akinyemi, wanda ya ce sun dade yana sauraron ranar da binciken zai soma, zalika tun a shekarar bara, tsohon shugaban ya bayyana cewa a shirye yake da ya amsa tambayoyi kan zargin.

A wani lamari na daban, Shugaban kasa Muhammadu Buhari yace dukkanin sakamakon zabe fara daga ranar Asabar 16 ga watan Fabrairu za su kasance na gaskiya da amana.

Garba Shehu, babban mai ba Shugaban kasa shawara a kafofin watsa labarai ne yace shugaba Buhari ya bayar da tabbacin ne a wani ganawa tare da sarakunan gargajiya a sakatariyar majalisar sarakunan a Yenagoa, Bayelsa da kuma Port Harcourt, Rivers a ranar Talata, 12 ga watan Fabrairu.

Sanarwa: Ku ci gaba da kasancewa tare da mu yayin da Shafin Naij.com Hausa ya sauya suna zuwa Legit.ng Hausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Domin shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.com

Ku biyo cikin shafukan mu na zaurukan sada zumunta:

https://facebook.com/legitnghausa

https://twitter.com/legitnghausa

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel