Da duminsa: Kotu ta baiwa Babachir David beli

Da duminsa: Kotu ta baiwa Babachir David beli

Wata babban kotun birnin tarayya Abuja ta baiwa tsohon sakataren gwamnatin tarayya, Babachir David Lawal, da wasu abokan laifinsa biyu beli.

Kotu a ranan Laraba ta baiwa Babachir David Lawal belin ne kan kudi N50m da mai tsaya masa guda daya. Wajibi ne mai tsaya masa ya kasance mazaunin birnin tarayya, ya nada filaye a Abuja, kuma ya gabatar da hujjan biyan haraji na shekaru uku.

Kotu ta kara da cewa kowanne daga cikinsu ya sallamar da fasfot dinsu har sai sun cika sharrudan belin kuma su cigaba da kasancewa hannun hukumar EFCC.

An daga zaman zuwa ranan 18 ga watan Febrairu, 2019.

Mun kawo muku cewa wata babbar kotun gwamnatin tarayya da ke da zama a Abuja, ta bayar da umurnin cewa tsohon sakataren gwamnatin tarayya, Mr Babachir Lawal, zai ci gaba da zama a hannun hukumar da ke yaki da cin hanci da rashawa da yiwa dukiyar gwamnati zagon kasa (EFCC).

KU KARANTA: Kotu ta baiwa IGP umurnin damke Walter Onnoghen

Hukumar tana zargin tsohon sakataren gwamnatin tarayyar da aikata laifuka 10 da suka shafi hada baki tare da sama da fadi da kudaden gwamnati, ta hanyar bayar da kwangilar bogi. Hukumar tana tuhumar Lawal ne tare da wasu mutane ukkuu da kamfanoni biyu.

Mutanen da kamfanonin da ake tuhumarsu tare da Lawal, sun hada da: Hamidu David Lawal; Sulaiman Abubakar; Apeh John Monday; kamfanin Rholavision Engineering Limited da kuma kamfanin Josmon Technologies Limited.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel