Ba zan baku kunya ba kamar APC - Atiku

Ba zan baku kunya ba kamar APC - Atiku

- Dan takarar Shugaban kasa a jam’iyyar PDP Atiku Abubakar, ya jadadda jajircewarsa na sauya fasalin lamuran kasar

- Atiku ya bayar da tabbacin cewa ba zai ba yan Najeriya kunya ba a alkawaran da ya daukar masu

- Ya sha alwashin mutunta kundin tsarin mulkin kasar

Dan takarar Shugaban kasa a jam’iyyar Peoples Democratic Party (PDP), Alhaji Atiku Abubakar, a jiya Talata, 12 ga watan Fabrairu ya jadadda jajircewarsa na sauya fasalin lamuran kasar.

Atiku ya bayar da tabbacin cewa ba zai ba yan Najeriya kunya ba a alkawaran da ya daukar masu kamar ya jam’iyyar All Progressives Congress (APC) mai mulki tayi.

Ba zan baku kunya ba kamar APC - Atiku

Ba zan baku kunya ba kamar APC - Atiku
Source: UGC

Da yake jawabi a gaban taron magoya bayansa a Lagas, Atiku ya caccaki gwamnatin APC akan zaga cikar alkawaran da ta daukar ma wadanda suka zabe ta kafin zaben 2015.

Atiku wanda ya sha alwashin mutunta kundin tsarin mulkin kasar yace: “Zan yi aiki tare da majalisar dokokin kasa domin kare bangaren shari’a da kuma mutunta doka da oda.

A halin da ake ciki, mun ji cewa Shugaban jam’iyyar Peoples Democratic Party (PDP), Uche Secondus, a ranar Talata, 12 ga watan Fabrairu yace babu makawa dan takarar Shugaban kasa na jam’iyyar, Alhaji Atiku Abubakar ya lashe zabe ya gama a zaben Shugaban kasa na ranar Asabar mai zuwa.

KU KARANTA KUMA: Zabe zai kasance na gaskiya da amana – Buhari ya sake bayar da tabbaci

Da yake jawabi a gangamin kamfen din Shugaban kasa na jam’iyyar a Lagas, Secondus yace babu mai hana dan takarar PDP.

Yace al’umma sun gaji da jam’iyyar All Progressives Congress (APC) mai mulki domin ganin ci gaban kasar.

Secondus ya kara da cewa yan Najeriya da yan kasashen waje da ke son ci gaban kasar sun yi watsi da APC inda suka aminta da Atiku.

Sanarwa: Ku ci gaba da kasancewa tare da mu yayin da Shafin Naij.com Hausa ya sauya suna zuwa Legit.ng Hausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Domin shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.com

Ku biyo cikin shafukan mu na zaurukan sada zumunta:

https://facebook.com/legitnghausa

https://twitter.com/legitnghausa

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel