Zaben 2019: Ba mu goyon bayan Atiku - Amurka ta mayarwa Keyamo martani

Zaben 2019: Ba mu goyon bayan Atiku - Amurka ta mayarwa Keyamo martani

- Gwamnatin kasar Amurka ta ce ba ta goyon bayan kowanne dan takara a zaben kujerar shugaban kasar Nigeria da za a gudanar a ranar 16 ga watan Fabreru

- Amurka ta bayyana cewar tallafin jin kai da ta ke baiwa Nigeria na sama da $1bn ba zai katse ba, ba tare da la'akari da wanda ya samu nasarar zaben ba

- Tun farko, Festus Keyamo, ya ce kasar Amurka ta fitar da maitarta a fili ta hanyar bada kariya da kuma goyon bayan Atiku Abubakar na jam'iyyar PDP

Gwamnatin kasar Amurka ta ce ba ta goyon bayan kowanne dan takara a zaben kujerar shugaban kasar Nigeria da za a gudanar a ranar 16 ga watan Fabreru, 2019.

Da ya ke Allah wadai da labaran da ake yadawa na cewar Amurka na goyon bayan wani dan takara, ofishin jakadancin kasar Amurka a Nigeria ya saki wata sanarwa na cewar tallafin jin kai da Amurka ke baiwa Nigeria na sama da $1bn ba zai katse ba, ba tare da la'akari da wanda ya samu nasarar zaben ba.

Tun farko, Festus Keyamo, kakakin kungiyar yakin zaben shugaban kasa Muhammadu Buhari, ya ce kasar Amurka ta fitar da maitarta a fili har duniya ta gani, ta hanyar bada kariya da kuma goyon bayan Atiku Abubakar na jam'iyyar PDP.

KARANTA WANNAN: Duk da barazanar El-Rufai: Burtaniya za ta turo wakilai 100 domin sa ido a zaben Nigeria

Zaben 2019: Ba mu goyon bayan Atiku - Amurka ta mayarwa Keyamo martani

Zaben 2019: Ba mu goyon bayan Atiku - Amurka ta mayarwa Keyamo martani
Source: Facebook

Keyamo ya ce Stuart Symington, Jakadan Amurka a Nigeria, "yana kokarin ya bayyana cewa PDP ce kadai zata iya lashe zabe idan har an yi sahihin zabe a kasar."

Amma a cikin wata sanarwa daga Symington a ranar Talata, Jakadan Amurkan ya bayyana cewa kasarsa ba ta goyon bayan kowanne dan takara, yana mai cewa Amurka na son a gudanar da sahihin takara kawai.

"Wannan zabe ne na Nigeria kuma 'yan Nigeria ne za su yanke hukunci kan wanda zai shugabanci kasar. Yana da matukar tasiri ga makomar Nigeria da mazauna cikinta kuma yana da muhimmanci wajen bunkasa demokaradiyya, zaman lafiya da kuma ganin cewa an gudanar da zaben cikin lumana da adalci.

"Hakan ne zai baiwa 'yan Nigeria damar ganin sahihin sakamakon zabe, wanda za su yi na'am da shi. Wannan zai daga darajar demokaradiyar Nigeria, kamar yadda ya yi a zaben 2015," a cewar sanarwar.

SANARWA: Shafin jaridar NAIJ.com Hausa ya sauya suna zuwa Legit.ng Hausa. Muna fatan za ka ci gaba da kasancewa tare da Legit.ng Hausa don karanta labarai da dumi duminsu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukan mu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel