Yanzu-yanzu: Kotu ta baiwa IGP umurnin damke Walter Onnoghen

Yanzu-yanzu: Kotu ta baiwa IGP umurnin damke Walter Onnoghen

Kotun ladabta ma'aikatan gwamnati, CCT, ta baiwa sufetan yan sanda, IG Mohammed Adamu, umurnin damke sallamammen shugaban alkalai, Walter Nkanu Onnoghen, kuma ya gurfanar da shi gaban kotun ranan Juma'a.

Yayinda aka koma sauraran karan a kotu, gwamnatin tarayya ta bukaci Alkalin kotun CCT ta bada umurnin damke Walter Onnoghen tun da ya ki zuwa kotun cikin lumana.

Lauyan gwamnati, Aliyu Umar, ya mika bukatar ne a ranan Laraba, 13 ga watan Febrairu, 2019 inda ya nuna bacin ransa kan taurin kan Walter Onnoghen.

Aliyu yace: "A halin da muke ciki yanzu, ina bukatar wannan kotun bisa ga dokarta ta S6(1), a bada umurnin damke abin zargi."

Shi kuma lauyan Onnoghen, Adegboyega Awomolo, ya bukaci kotun kada ta amsa wannan bukata saboda dalilai da dama.

Amma alkalin kotun CCT, Jastis Danladi Umar, tare da wasu alakai biyu sunyi watsi da bukatar lauyan Onnoghen kuma suka baiwa jami'an tsaro umurnin kawo Onnoghen kotun ranan Juma'a.

Yace: "Ina son in ga abin zargi (Walter Onnoghen) cikin akwatin laifi ranan Juma'a"

KU KARANTA: Buhari, Atiku sun isa wajen rattaba hannu kan takardan lumana

Shugaba Muhammadu Buhari ya nada sabon Alkalin alkalai mai suna Jastis Ibrahim Tanko Mohammed.

Gwamnatin shugaba Buhari tana tuhumtar Jastis Onnoghen da laifin rashin bayyana wasu kudade a asusun banki shida duk da kasancewarsa ma'aikacin gwamnati.

Gwamnatin tarayyar Najeriya ta umurci hukumar leken asirin kudaden sata wato Nigerian Financial Intelligence Unit (NFIU) da ta daskarar da asusun bankin shugaban Alkalan Najeriya, Jastis Walter Onnoghen, guda biyar.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel