Zabe zai kasance na gaskiya da amana – Buhari ya sake bayar da tabbaci

Zabe zai kasance na gaskiya da amana – Buhari ya sake bayar da tabbaci

- Shugaban kasa Buhari yace dukkanin sakamakon zabe fara daga ranar Asabar 16 ga watan Fabrairu za su kasance na gaskiya da amana

- Buhari ya bayar da tabbacin ne a wani ganawa tare da sarakunan gargajiya a sakatariyar majalisar sarakunan a Yenagoa

- Ya yaba da tsarin amfani da katin zabe da kuma na’urar Card Reader, sannan ya bukaci mutanen kasar da su rungumi kimiya

Shugaban kasa Muhammadu Buhari yace dukkanin sakamakon zabe fara daga ranar Asabar 16 ga watan Fabrairu za su kasance na gaskiya da amana.

Garba Shehu, babban mai ba Shugaban kasa shawara a kafofin watsa labarai ne yace shugaba Buhari ya bayar da tabbacin ne a wani ganawa tare da sarakunan gargajiya a sakatariyar majalisar sarakunan a Yenagoa, Bayelsa da kuma Port Harcourt, Rivers a ranar Talata, 12 ga watan Fabrairu.

Zabe zai kasance na gaskiya da amana – Buhari ya sake bayar da tabbaci

Zabe zai kasance na gaskiya da amana – Buhari ya sake bayar da tabbaci
Source: Twitter

Shugaba Buhari yace: “Na baku tabbacin cewa na shirya ma zabe na gaskiya da amana. Hukumar zabe mai zaman kanta (INEC) ta san matsaya na akan haka.

“Ina ba yan Najeriya tabbacin zabe na gaskiya da amana. A karkasin wannan shugabanci, babu wanda za a bari ya yiwa sauran al’umma barazana.

KU KARANTA KUMA: Zabe: Yan sanda sun gargadi yan siyasa akan siyan kuri’u

“Babu wanda za a bari ya kwace akwatunan zabe sannan ya gudu dasu. Zan tabbatar da ganin kuri’u kowa ya yi amfani.”

Ya yaba da tsarin amfani da katin zabe da kuma na’urar Card Reader, sannan ya bukaci mutanen kasar da su rungumi kimiya, inda ya bayyana cewa idan ba don su ba da ba a kawo karsen mulkin zalunci na shekaru 16 ba.

Sanarwa: Ku ci gaba da kasancewa tare da mu yayin da Shafin Naij.com Hausa ya sauya suna zuwa Legit.ng Hausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Domin shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.com

Ku biyo cikin shafukan mu na zaurukan sada zumunta:

https://facebook.com/legitnghausa

https://twitter.com/legitnghausa

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel