Yanzu-yanzu: Buhari, Atiku sun isa wajen rattaba hannu kan takardan lumana

Yanzu-yanzu: Buhari, Atiku sun isa wajen rattaba hannu kan takardan lumana

Yan takaran kujeran shugaban kasan Najeriya karkashin jam'iyyar Peolples Demcratic Party PDP, da na jam'iyyar All Progressives Congress APC, Atiku Abubakar da shugaba Muhammadu Buhari sun rattaba hannu kan takardan lumana a dakin taron International Conference Center ICC dake birnin tarayya Abuja.

Manyan yan siyasan biyu sun hadu a lokaci daya karo na farko tun lokacin da suka fara yakin neman zabe ne domin rattaba hannu kan takardan lumana gabanin zaben ranan Asabar.

Yanzu-yanzu: Buhari, Atiku sun isa wajen rattaba hannu kan takardan lumana

Yanzu-yanzu: Buhari, Atiku sun isa wajen rattaba hannu kan takardan lumana
Source: Facebook

Daga cikin wadanda ke halarce a taron sune sakataren kasashen Commonwealth, Patricia Scotland; tsohon shugaban kasa, Janar AbdusSalam Abubakar; da sauran mambobin kwamitin zaman lafiya.

Bayan isowar yan takaran, Janar Abubakar ya yi kira ga masu ruwa da tsaki a wannan zaben da su tabbatar da zaman lafiya kafin zabe da bayan zabe.

Ya yi kira da yan takara suyi amfani da kwanaki da suka rage domin magana da jama'a da magoya bayansu sabanin soke-soken juna. Ya yi bayanin cewa yana jaddada haka ne saboda a daina bukatar gayyatan yan kasashen waje a zaben gaba.

Yanzu-yanzu: Buhari, Atiku sun isa wajen rattaba hannu kan takardan lumana

Yanzu-yanzu: Buhari, Atiku sun isa wajen rattaba hannu kan takardan lumana
Source: Facebook

Atiku Abubakar ya zo tare da shugaban jam'iyyar PDP, Uche Secondus, shugaban majalisar dattawa, Bukola Saraki, da wasu jiga-jigan jam'iyyar.

Hakazalika shugaba Buhari ya isa taron tare da shugaban jam'iyyar APC, Adams Oshiomole, tare da wasu manyan jami'an gwamnati.

Yanzu-yanzu: Buhari, Atiku sun isa wajen rattaba hannu kan takardan lumana

Yanzu-yanzu: Buhari, Atiku sun isa wajen rattaba hannu kan takardan lumana
Source: Facebook

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel