Duk da barazanar El-Rufai: Burtaniya za ta turo wakilai 100 domin sa ido a zaben Nigeria

Duk da barazanar El-Rufai: Burtaniya za ta turo wakilai 100 domin sa ido a zaben Nigeria

- Gwamnatin kasar Burtaniya ta ce za ta tura sama da wakilai 100 a jihohi akalla 15, domin sa ido kan yadda zabukan ranar Asabar zai kasance

- UK ta ce za ta ci gaba da girmama kasar Nigeria a matsayin mai cin kashin kanta amma za ta kasance mai tallafa mata wajen bunkasa demokaradiyyarta

- Burtaniya ta jaddada cewa tana da yakinin cewa an shirya abubuwa da dama domin ganin cewa an gudanar da sahihin zabe da ya zarce na 2015

Gwamnatin kasar Burtaniya ta ce za ta tura sama da wakilai 100 a jihohi akalla 15, domin sa ido kan yadda zabukan ranar Asabar, 16 ga watan Fabreru, 2019 zai kasance.

Catriona Laing, jakadiyar kasar Burtaniya a nan Nigeria, ta bayyana hakan a ranar Talata a lokacin da ta ke yin bayani kan yunkurin Burtaniya na tallafawa Nigeria wajen ganin an gudanar da sahihin zabe a kasar.

Laing ta ce UK za ta ci gaba da girmama kasar Nigeria a matsayin mai cin kashin kanta amma za ta kasance mai tallafa mata wajen bunkasa demokaradiyyarta.

KARANTA WANNAN: Hukuncin kotu: Gwamnatin Nigeria ba ta da ikon rufe asusun bankin Onnoghen

Duk da barazanar El-Rufai: Burtaniya za ta turo wakilai 100 domin sa ido a zaben Nigeria

Duk da barazanar El-Rufai: Burtaniya za ta turo wakilai 100 domin sa ido a zaben Nigeria
Source: Twitter

Da ta ke jawabi a matsayin bakuwa ta musamman a wani shirin wayar da kan 'yan Nigeria da gidan Rediyo na NIFM Abuja ke gabatarwa, jakadiyar ta ce: "A matsayinmu na masu sa ido a kashin kasu, muna girmama Nigeria a matsayin klasa maim cin kashin kanta; ya zamar mana wajibi mu kasance da jama'ar Nigeria domin cimma muradunta na demokaradiyya.

"Yadda za a gudanar da zaben ne babbar damuwarmu. Wannan ne dalilin da ya sanya zamu tura wakilanmu sama da 100 zuwa jihohi 15 domin bunkasa sa ido ga wakilan kungiyar kasashen turai, da na Amurka, da ma na cikin kasar baki daya.

"Muna da yakinin cewa an shirya abubuwa da dama domin ganin cewa an gudanar da sahihin zabe da ya zarce na 2015. Mun saka jari mai tsoka a matsayin abokiyar hulda da hukumar zabe mai zaman kanta ta kasa INEC da kuma kungiyoyin fararen hula domin bunkasa hukumar da kuma hanyoyin gudanar da zabe."

SANARWA: Shafin jaridar NAIJ.com Hausa ya sauya suna zuwa Legit.ng Hausa. Muna fatan za ka ci gaba da kasancewa tare da Legit.ng Hausa don karanta labarai da dumi duminsu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukan mu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel