16 ga watan Fabrairu: Babu mai hana Atiku – Secondus

16 ga watan Fabrairu: Babu mai hana Atiku – Secondus

Shugaban jam’iyyar Peoples Democratic Party (PDP), Uche Secondus, a ranar Talata, 12 ga watan Fabrairu yace babu makawa dan takarar Shugaban kasa na jam’iyyar, Alhaji Atiku Abubakar ya lashe zabe ya gama a zaben Shugaban kasa na ranar Asabar mai zuwa.

Da yake jawabi a gangamin kamfen din Shugaban kasa na jam’iyyar a Lagas, Secondus yace babu mai hana dan takarar PDP.

Yace al’umma sun gaji da jam’iyyar All Progressives Congress (APC) mai mulki domin ganin ci gaban kasar.

Secondus ya kara da cewa yan Najeriya da yan kasashen waje da ke son ci gaban kasar sun yi watsi da APC inda suka aminta da Atiku.

16 ga watan Fabrairu: Babu mai hana Atiku – Secondus

16 ga watan Fabrairu: Babu mai hana Atiku – Secondus
Source: UGC

Shugaban jam’iyyar ya bayyana cewa tarin goyon baya da Atiku ya samu daga yan Najeriya a fadin kasar, mussamman a wuraen kamfen ya nuna karara cewa zai yi nasara.

Secondus yace sauya shugabannin yan sanda da akayi gabannin zabe a jihohi irin Lagas da Kwara duk zakuwa ne irin da gwamnati mai ci.

KU KARANTA KUMA: Hotunan Zahra da Yusuf Buhari suna yiwa mahaifinsu kamfen a Abuja

Ya yi zargin cewa suya sabbin kwamishinonin yan sanda da aka yi a wadannan jia duk don magudin sakamakon zabe ne.

Secondus ya kuma kara da cewa PDP za ta dakile duk wani shiri na sauya burin mutane.

Sanarwa: Ku ci gaba da kasancewa tare da mu yayin da Shafin Naij.com Hausa ya sauya suna zuwa Legit.ng Hausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Domin shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.com

Ku biyo cikin shafukan mu na zaurukan sada zumunta:

https://facebook.com/legitnghausa

https://twitter.com/legitnghausa

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel