Buhari, Atiku za su kulla yarjejeniyar amincewa da yadda sakamakon zabe zai kasance

Buhari, Atiku za su kulla yarjejeniyar amincewa da yadda sakamakon zabe zai kasance

A yau Laraba dan takarar kujerar shugaban kasa na jam'iyyar PDP, Atiku Abubakar, da shugaban kasa Muhammadu Buhari, dan takara na jam'iyyar APC, za su kulla yarjejeniya ta amincewa da duk yadda sakamakon babban zaben kasa zai kasance.

Da sanadin shafin jaridar Daily Trust mun samu rahoton cewa, a yau Laraba dan takarar kujerar shugaban kasa na jam'iyyar PDP, Atiku Abubakar, da kuma dan takara na jam'iyyar APC, shugaban kasa Muhammadu Buhari, za su rattaba hannu kan yarjejeniyar tabbatar da zaman lafiya tare da amincewa da duk yadda sakamakon zabe ya kasance.

Buhari, Atiku za su kulla yarjejeniyar amincewa da yadda sakamakon zabe zai kasance

Buhari, Atiku za su kulla yarjejeniyar amincewa da yadda sakamakon zabe zai kasance
Source: Facebook

Majiyar jaridar Legit.ng ta ruwaito cewa, shugaban kasa Buhari da babban abokin adawar su za su gana a yau cikin garin Abuja domin tabbatar da wannan yarjejeniya dangane da sakamakon zaben kasa da za a gudanar a ranar Asabar, 16 ga watan Fabrairu.

A yayin tuntubar fadar shugaban kasa dangane da wannan babban lamari, mai magana da yawun shugaban kasa Buharim Mista Femi Adesina ya bayar da tabbacin cewa Ubangidan sa zai halarci taron na kulla aminci kan sakamakon zaben bana.

KARANTA KUMA: APC za ta gudanar da taron yakin zabe a garin Abuja, PDP ta janye na ta

Kazalika, babban hadimi na musamman ga tsohon mataimakin shugaban kasa akan hulda da al'umma, Mista Paul Ibe, ya ce ba bu abinda zai hana Atiku rattaba kan yarjejeniyar tabbatar da zaman lafiya da tawakkali kan duk yadda sakamakon babban zaben ya kasance.

Jaridar Legit.ng ta ruwaito cewa, shugaban kasa Buhari da sauran 'yan takara masu hankoron kujerar shugaban kasa, sun rattaba hannu tare da kulla yarjejeniyar tabbatar da zaman lafiya da kwanciyar a ranar 11 ga watan Dasumba na shekarar da ta gabata.

Sanarwa: Ku ci gaba da kasancewa tare da mu yayin da Shafin Naij.com Hausa ya sauya suna zuwa Legit.ng Hausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Domin shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.com

Ku biyo cikin shafukan mu na zaurukan sada zumunta:

https://facebook.com/legitnghausa

https://twitter.com/legitnghausa

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel