Gwamnatin Tarayya ta dakatar da duk wani matakin shari'ah da take dauka kan Onnoghen - NBA

Gwamnatin Tarayya ta dakatar da duk wani matakin shari'ah da take dauka kan Onnoghen - NBA

- Kungiyar lauyoyin kasar nan sunyi kira ga gwamnati data dakatar da tuhumar da takeyiwa shugaban alkalan kasar nan

- Ganin CJN a kantar tsare masu laifi zai zama abun kaskantarwa a garemu

- Sun nemi gwamnati data mika binciken hannun masajisar alkalai ta kasa (NJC)

Gwamnatin Tarayya ta dakatar da duk wani matakin shari'ah da take dauka kan Onnoghen - NBA

Gwamnatin Tarayya ta dakatar da duk wani matakin shari'ah da take dauka kan Onnoghen - NBA
Source: Twitter

Kungiyar lauyoyi ta Najeriya (NBA) ta kara yin kira ga bangaren zabbabun gwamnatin tarraya dasu dakatar da tuhumar da suke yiwa shugaban alkalai na Najeriya(CJN) Justice Walter Onnoghen.

Shugaban kungiyar ta (NBA) Mr Paul Usoro ne ya bayyana hakan a ranar Talata a Abuja.

"Ganin CJN a kantar tsare masu laifi zai zama kaskantarwa a garemu da ita kanta gwamnatin"

"Muna shawartar gwamnati data mika wannan abu hannun majalisar alkalai ta kasa(NJC) wanda tuntuni suka bada amsar su".

Ya kara da cewa hanyoyin da NJC zasubi zai bada damar gano bakin zaren akan tuhumar da ake yiwa CJN ,sannan idan aka gano cewar yana da laifi NJC zasu yanke masa hukuncin daya kamata.

GA WANNAN: Hayaniya, fushi da cece-kuce bayan da aka yiwa soji 200 ritaya

Wanda hukuncin zai iya kasancewa kora ko kuma ajjiye aikin.

"Bayan bawa NJC wannan dama daga wannan lokaci bazai iya yin wani aiki ba a matsayin CJN sannan kuma kowacce hukumar bincike zata iya gudanar da aikinta a kanshi dama sauran kotuna".

Daga karshe Usoro ya roki da a dakatar da mika wannan batu ga CCT a ranar Laraba.

Shafin NAIJ.com Hausa ne ya koma LEGIT.ng Hausa

Latsa kuga sabuwar manhajar Legit.ng Hausa a wayarku ta salula: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Shafukanmu na dandalin sada zumunta sune:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel