Matasan Yarabawa sunce bassu tare da kungiyar dattijansu ta Afenifere masu son Atiku

Matasan Yarabawa sunce bassu tare da kungiyar dattijansu ta Afenifere masu son Atiku

- Wani bangare na Afenifere sun nuna goyon bayan su ga Buhari

- Kungiyar matasan tace ta gamsu da tsaro, fada da rashawa, habaka tattalin arziki da samar da ababen more rayuwa da gwamnatin shi tayi

- Kungiyar tayi kira ga masu fadi aji a Najeriya dasu kade kunnen su akan masu kira ga hargitsi yayin zabe

Matasan Yarabawa sunce bassu tare da kungiyar dattijansu ta Afenifere masu son Atiku

Matasan Yarabawa sunce bassu tare da kungiyar dattijansu ta Afenifere masu son Atiku
Source: Facebook

A shirin zabeb asabar mai zuwa na shugabancin kasa, wata kungiyar matasa daga kudu maso yamma ta soke goyon bayan Dan takarar PDP Atiku Abubakar.

Matasan masu magana karkashin zauren matasan kudu maso yamma sun koma goyon bayan shugaban kasa Muhammadu Buhari, wanda wani bangaren ta ne karkashin jagorancin Pa Ayo Fasanmi sukayi hakan.

Matasan Yarabawa sunce bassu tare da kungiyar dattijansu ta Afenifere masu son Atiku

Matasan Yarabawa sunce bassu tare da kungiyar dattijansu ta Afenifere masu son Atiku
Source: Depositphotos

Majiyar mu ta ruwaito cewa wani bangaren Afenifere ta mika wuya ga Buhari lokacin da ya kai ziyarar kamfen jihar Legas a ranar asabar.

A karshen taron zauren, matasan sun nuna goyon bayan su ga Buhari saboda ya cika alkawarin shi na 2015 a don haka ne ya cancanci a zabe shi.

Wannan jawabin na kunshe ne a takardar da suka bada a karshen taron ga majiyar tamu.

Kamar yanda kungiyar tace, Asiwaju Bola Tinubu, shugaban APC na kasa har yau shine murya, jagora kuma mai kishin yarbawa. Kishin yarbawa da yakeyi har yau ba a samu dan siyasa mai irin shi ba.

GA WANNAN: EFCC ta sake chafko matasa masu zambo cikin aminci su 11

Shugaban kungiyar, Prince Foluso Ajimuda, mashiryin yankin kudu maso yamma, Engr Biola Otun Coker da sakatare, Comrade Adeola Akinjeji ne suka saka hannu a takardar.

Kungiyar tace ta jinjinawa Buhari akan kokarin da yayi a fannin tsaro, yaki da rashawa, habaka tattalin arziki da cigaba ta hanyar samar da ababen more rayuwa.

Ta nuna yakinin ta get na cewa mulkin Buhari zai samar da damar yin zabe mai yanci, cike kuma da zaman lafiya da lumana.

Matasan sunyi kira ga masu fadi aji a Najeriya dasu yi biris da makiya damokaradiyya dake kira don fada da hargitsi ya tashi.

Shafin NAIJ.com Hausa ne ya koma LEGIT.ng Hausa

Latsa kuga sabuwar manhajar Legit.ng Hausa a wayarku ta salula: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Shafukanmu na dandalin sada zumunta sune:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel