N200m suke so a biya su kafin su sako dan takarar APC da suka sace

N200m suke so a biya su kafin su sako dan takarar APC da suka sace

- Wadanda sukayi garkuwa da daraktan kamfen din dan takarar Majalisar wakilai na Ovia ta kudu sun bukaci Naira miliyan 200

- Dan takarar Mr Dennis ya danganta garkuwar da wani nau'i na siyasa

- Yace burin canza Ovia na mutanen yankin ne, babu kuma wanda zai iya canza musu ra'ayi

N200m suke so a biya su kafin su sako dan takarar APC da suka sace

N200m suke so a biya su kafin su sako dan takarar APC da suka sace
Source: Facebook

Wadanda sukayi garkuwa da Mr Monday Aighobhahi, Darakta Janar din kamfen din dan takarar majalisar wakilai na Ovia jihar Edo karkashin jam'iyyar APC sun bukaci kudin fansa har Naira miliyan 200 don sakin shi.

Dan takarar majalisar wakilai a APC, Mr Dennis Idahosa, Wanda ya zargi masu garkuwa da daraktan nashi a matsayin yan siyasa, ya sanar da manema labarai a Benin City cewa masu garkuwar sun same shi ne awoyi biyu bayan sace daraktan.

"Eh, sun kira ni wajen karfe 9 daren kuma sai suka kara kira da safen nan inda suke jaddada cewa sai an biya Naira miliyan 200 kafin su saki Aighobhahi,"

GA WANNAN: Naira ta dan hau kadan kan dala, amma kuma har yanzu tana shan mari daga manya

"Na gano manufar wadannan mutanen amma sun fadi, yunkurin canza Ovia ba wai Idahosa ne kadai, burin mutanen ne kuma basu isa su kashe shi ba," inji shi.

Aighobhahi an sace shi ne a babbar hanyar Benin-Ore a ranar talata, jim kadan bayan gama kamfen a karamar hukumar Ovia ta kudu na jihar.

Aighobhahi, tsohon shugaban karamar hukumar Ovia ta kudu maso yamma, an sace shi ne tare da Mr Mike Ogiamen, shugaban gundumar Ugbogui.

Shafin NAIJ.com Hausa ne ya koma LEGIT.ng Hausa

Latsa kuga sabuwar manhajar Legit.ng Hausa a wayarku ta salula: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Shafukanmu na dandalin sada zumunta sune:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Mailfire view pixel