Wannan zaben yafi kowanne razana ni - Prof. Bolaji Akinyemi

Wannan zaben yafi kowanne razana ni - Prof. Bolaji Akinyemi

- Prof Bolaji Akinyemi yace zaben shekara ta 2019 shine zaben daya taba sanyashi cikin fargaba

- Zabe yana kara gabatowa ina kara shiga cikin fargaba

- Ba'a tabayin wani zabe daya sanyani cikin fargaba ba sama da wannan zaben mai zuwa

Wannan zaben yafi kowanne razana ni - Prof. Bolaji Akinyemi

Wannan zaben yafi kowanne razana ni - Prof. Bolaji Akinyemi
Source: Depositphotos

Bisa ga karatowar zaben shekara ta 2019 wanda ya rage saura kwanaki Shida Prof Bolaji Akinyemi tsohon ministan kula da harkokin cikin gida ya bayyana cewa yana cikin fargabar wannan zabe.

"Tunda da nake kula da zabe a Najeriya bazan iya tuna wane zabe ne ya sanyani cikin fargaba ba sama da wannan zabe mai zuwa".

Akinyemi ya bayyana hakan ne a ranar Lahadin data gabata sannan ya kara da nuna damuwar sa musamman a bangaren takarar shugaban kasa wanda ya hada da shugaban kasa Muhammad Buhari na jam'iyar APC da kuma tsohon mataimakin shugaban kasa Atiku Abubakar na jam'iyar PDP.

GA WANNAN: Yadda tattalin arzikin Najeriya ya habaka a bara 2018

Sannan ya bayyanawa shuwagabannin siyasar Najeriya dasu rinjayi magoya bayan su ta hanyar hana tada hargitsi da kwaucewa duk wani aby daya sabawa da damukradiyya a lokacin gudanar da zabe.

Akinyemi ya kara da cewa lokaci yazo da shugabanni da magoya bayansu zasu dinga karbar duk wani sakamako da aka fitar na zabe idan har suna duba ne fata na gaskiya da kuma kudirin masu zaben.

Shafin NAIJ.com Hausa ne ya koma LEGIT.ng Hausa

Latsa kuga sabuwar manhajar Legit.ng Hausa a wayarku ta salula: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Shafukanmu na dandalin sada zumunta sune:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel