Masu garkuwa da mutane sun kashe wani babban Fasto, sun yi awon gaba da iyalansa a Zamfara

Masu garkuwa da mutane sun kashe wani babban Fasto, sun yi awon gaba da iyalansa a Zamfara

Wani babban faston cocin Anglican, Anthony Jatau ya gamu da ajalinsa a hannun wasu gungun yan bindiga a jahar Zamfara a daidai lokacin da yake kan hanyarsa ta komawa sabon wurin aikinsa a jahar Katsina, inji rahoton jaridar Punch.

Majiyar Legit.ng ta ruwaito baya da kashe Jatau, yan bindigan sun yi awon gaba da matarsa, yayansa da kuma kannen matarsa guda biyu mata da nufin yin garkuwa dasu har sai an biyasu kudaden fansa kafin su sakesu.

KU KARANTA: Babbar kotu ta garkame shugaban bankin Ecobank akan satar naira miliyan 411

Hukumar cocin Anglican shiyyar Sakkwato ce ta sauya ma Jatau wurin aiki, inda ta daukeshi daga cocinta dake garin Gusau zuwa cocinta dake jahar Katsina, amma yana kan hanyarsa ta komawa Katsinan ne yan bindigan suka bude masa wuta.

A sakamakon haka ne suka bindigeshi, sa’annan motar ta kufce masa, wanda hakan yasa motar ta koma zuwa gefen hanya, haka dai suka bi motar har suka ciro gawarsa daga cikinta, suka jefar da ita a gefen hanya, sa’annan suka kada sauran iyalansa dake cikin motar zuwa cikin daji.

Wata majiya daga Cocin Anglican Sakkwato ta tabbatar da faruwar lamarin, inda tace zuwa yanzu yan bindigan sun kira waya, inda suka nemi cocin ta biyasu kudi naira miliyan goma kafin su sako matarsa, yayansa da kuma surukannasa.

“Dukkanmu muna cikin bacin rai da alhini, tare da tunanin halin da iyalansa ke ciki a hannun yan bindigan, cocinmu bata da wannan makudan kudin da suke nema, amma dai muna sa ran tara dan abinda zamu iya don ganin an sakosu duka.

“A yanzu haka duk mun shiga cikin rudani, sakamakon lokacin da suka bamu yana tafiya, kuma bamu san abinda zasu aikata anan gaba ba, kuma mun sanar da jami’an tsaro, amma dai babu wani cigaba har yanzu.” Inji shi.

Duk kokarin da majiyarmu tayi na jin ta bakin kaakakin rundunar Yansandan jahar, Mohammed Shehu yaci tura, sakamakon yayi alkawarin bata karin bayani, amma har lokacin tattara wannan rahoto bai tuntubeta ba.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel