APC za ta gudanar da taron yakin zabe a garin Abuja, PDP ta janye na ta

APC za ta gudanar da taron yakin zabe a garin Abuja, PDP ta janye na ta

Da sanadin shafin jaridar Daily Trust mun samu cewa, akwai yiwuwar samun cinkoson al'umma tare da jerin gwanon Motoci yayin taron yakin neman zaben kujerar shugaban na jam'iyyar APC da za a gudanar a yau Laraba cikin babban birnin kasar nan na tarayya.

A yayin da a yau babbar jam'iyyar adawa ta PDP ta shirya gudanar da taron ta na yakin neman zaben kujerar shugaban kasa cikin garin Abuja, jam'iyya mai ci ta APC ta yi kakagida wajen tilastawa jam'iyyar ta hamayya janye na ta taron da kudirci gudanarwa.

APC za ta gudanar da taron yakin zabe a garin Abuja, PDP ta janye na ta

APC za ta gudanar da taron yakin zabe a garin Abuja, PDP ta janye na ta
Source: UGC

Jam'iyyar PDP na ci gaba da zargin gwamnatin shugaban kasa Muhammadu Buhari da ke jagorancin kasar nan a karkashin inuwa ta jam'iyyar APC da mulki na kama karya yayin da ta haramta ma ta gudanar da taron ta cikin garin Abuja a makon da ya gabata.

Majiyar jaridar Legit.ng ta ruwaito cewa, an tsananta tsaro a garin Abuja yayin da jiga-jigan jam'iyyar APC na kasa da kuma gwamnonin kimanin 22 na jam'iyyar za su halarci taron yakin neman zabe yayin da shugaban kasa Buhari zia gabatar da jawaban sa a yau 13 ga watan Fabrairu.

KARANTA KUMA: Gwamnan Jihar Bauchi ya yi rashin wani dan uwan sa na jini

Masu sharhi akan harkokin siyasa sun yi zargin cewa, jam'iyya mai ci ta APC ta shirya gudanar da taron ta na yakin zabe a yau cikin garin Abuja domin haramtawa jam'iyyar adawa PDP gudanar da na ta taron a babbar fada ta shugabancin kasar nan.

Jaridar Legit.ng ta ruwaito cewa, a makon da ya gabata ne dan takarar kujerar shugaban kasa na jam'iyyar PDP, Atiku Abubakar, ya shirya gudanar da taron sa na yakin neman zabe a harabar filin fareti da ke garin Abuja.

Sanarwa: Ku ci gaba da kasancewa tare da mu yayin da Shafin Naij.com Hausa ya sauya suna zuwa Legit.ng Hausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Domin shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.com

Ku biyo cikin shafukan mu na zaurukan sada zumunta:

https://facebook.com/legitnghausa

https://twitter.com/legitnghausa

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel