Mutane 3 sun sheka barzahu yayin arangama tsakanin Yansanda tsagerun IPOB a Imo

Mutane 3 sun sheka barzahu yayin arangama tsakanin Yansanda tsagerun IPOB a Imo

Akalla mutane uku ne aka kashe a garin Owerri na jahar Imo yayin da yayan kungiyar tsageru masu rajin kafa kasar Biyafara ta IPOB suka yi wata kazamar arangama da jami’an rundunar Yansandan Najeriya a ranar Litinin, 11, ga watan Feburairu.

Majiyar Legit.ng ta ruwaito wani jami’in Dansanda da bai yadda a bayyana sunansa ba ya shaida mata cewa jerin gwanon yayan kungiyar IPOB ne suka far ma duk wata fasta da allunan hotunan yan siyasa dake kan titin Okigwe, suna farfasasu tare yagasu.

KU KARANTA: Babbar kotu ta garkame shugaban bankin Ecobank akan satar naira miliyan 411

Mutane 3 sun sheka barzahu yayin arangama tsakanin Yansanda tsagerun IPOB a Imo

Tsagerun IPOB
Source: Twitter

Ba tare da wata wata ba rundunar Yansanda ta tura jami’anta don shawo kan matsalar, sai dai isarsu keda wuya sai tsagerun IPOB din suka ce “da wa Allah ya hadamu in ba ku ba” suka diran ma Yansandan.

“Wannan ne dalilin da yasa Yansandan suka bude musu wuta, inda nan take mutane uku daga cikin tsagerun suka fadi matattu, yayin da wasu guda biyu suka samu munanan rauni, wanda hakan yasa yan uwansu suka garzaya dasu Asibiti, daga bangaren Yansanda ma an samu mutane hudu da suka jikkata.” Inji shi.

Haka zalika wata majiyar ta daban ta bayyana cewa daga cikin sauran tsagerun IPOB da suka tsere, akwai wanda ya kwace bindigan Dansanda guda daya kirar AK-47, sa’annan ya kara da cewa daga bisani kwamandan Yansandan yaki da fashi da makami, Victor Geoffery ya tura jami’ansa zuwa wurin.

“Kwamanda Geoffery ta tura Yansandan dake yaki da yan fashi da makami zuwa wurin da aka samu rikicin, inda suka samu nasarar kama wasu yayan kungiyar ta IPOB da adadinsu ya kai ashirin, tare da kama tutocin Biyafara.” Inji shi.

Daga karshe kwamishinan Yansandan jahar, Dasuki Galadanci ya tabbatar da faruwar hatsaniyar, sa’annan ya tabbatar da kama tsagerun, kuma ya bada tabbacin zasu gurfanar dasu gaban kuliya manta sabo da zarar sun kammala gudanar da bincike.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel