Naira ta dan hau kadan kan dala, amma kuma har yanzu tana shan mari daga manya

Naira ta dan hau kadan kan dala, amma kuma har yanzu tana shan mari daga manya

- N361.67 nairar take kokartawa a kan kowacce dala

- Dalar ta wahal da Naira a shekarun nan

- Sai ka tara naira daidai-dai a kullum shekara guda zaka sami dala 1

Naira ta dan hau kadan kan dala, amma kuma har yanzu tana shan mari daga manya

Naira ta dan hau kadan kan dala, amma kuma har yanzu tana shan mari daga manya
Source: Depositphotos

A kasuwar hada-hadar musayar kudade ta Naira da Dala, Pam da Yuro, Nairas ta dan sami tagomashi na 'yan kwabbai a jiya a kasuwar musayar, inda ta hau kan dalar kadan da kwabbai 28, watai N361.67 ga kowacce dala.

A litinin dai, N361.95 ce ake karbar dalar da ita, wanda ya nuna naira tana dan kara samun kariya, kuma tana kan dawowa yadda take a shekarun baya.

A kasuwannin bayan fage na Legas kuwa, Nairas ta kai N358 a kan dala wadda ke nuna dalar tana dan wuya wajen samuwa ahannun mutane, tunda kowa can yake zuwa wurin masu sayarwa a titi, ba banki ba.

GA WANNAN: Waiwaye a Kannywood, jerin hotuna da sunayen aftawa da suka rasu a shekaru 20, mata da maza

Naira dai, a lokacin PDP tana 164 ne, inda daga kan 2015 ta koma 198 kan kowacce dala.

Saidai faduwar farashin man fetur, da ma rufe dukkan kudaden gwamnati da shugaban kasa yasa ayi, ya kai nairas har N500 a 2016, kafin daga baya a sami dalar a hannun gwamnati, lokacin da Osinbajo ya dan karbi mukaddasanci na wucen gadi, ya kuma bari a sayarda dalar, ta daidaita a 365 shekaru biyu.

A lissafi gwari-gwari dai, sai ka tara N1 a kullum kana ajjewa shekara guda, kafin ka ajje dala daya, watau N365 a kan dala $1 cikin kwanaki 365.

Farashin BDC dai, cewa yayi a sayar da dala a N360, Pam na Ingila a kan N473, sai Yuro na Turai a kan N411.

Shafin NAIJ.com Hausa ne ya koma LEGIT.ng Hausa

Latsa kuga sabuwar manhajar Legit.ng Hausa a wayarku ta salula: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Shafukanmu na dandalin sada zumunta sune:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel