Kaje gida ka huta! Baka bukatar aiki bayan ritaya - Junaid ga dattijo Buhari

Kaje gida ka huta! Baka bukatar aiki bayan ritaya - Junaid ga dattijo Buhari

- Tsohon hadimin shugaban Najeriya, dan siyasa Dr Junaid Muhammad yace shugaba Buhari ya komai gida ya huta domin a bayyane yake cewar bazai iya tafi da kasa Nigeria ba

- Ya bukaci Buhari da yaje a cigaba da mai da hankali akan lafiyarsa ya kyale wasu su wadanda zasu iya suyi mulki

Kaje gida ka huta! Baka bukatar aiki bayan ritaya - Junaid ga dattijo Buhari

Kaje gida ka huta! Baka bukatar aiki bayan ritaya - Junaid ga dattijo Buhari
Source: Depositphotos

Dr Junaid Muhammad, dan siyasa kuma hadimi ga tsohon shugaban Najeriya, yace shugaba Buhari ya komai gida ya huta domin a bayyane yake cewar bazai iya tafi da kasa Nigeria ba.

Ya bukaci Buhari da yaje a cigaba da mai da hankali akan lafiyarsa ya kyale wasu su wadanda zasu iya suyi mulki.

Yace idan har aka bari Buhari ya zarce a zaben 2019 to tabbas rigingimu da ake zasu cigaba da karu wa musamman rigingimu tsakanin makiyaya da manoma fiye da yadda ba a zato .

Mohammed wanda yace yana cikin manyan arewa mafi kusanci da Buhari amma ya tabbatar da cewa buhari ba zai iya mulkin nan ba domin ba ya mulki a irin tsarin da ya dace.

Ya kara da cewa Buharin yafi maida hankali ga rayuwar iyalinsa akan ta 'yan Nigeria, ya bar abokansa da ragamar harkar tattalin arzikin kasa wanda hakan yake janyo matsalar tattalin arziki ta kara tabarbarewa.

GA WANNAN: Hayaniya, fushi da cece-kuce bayan da aka yiwa soji 200 ritaya

Dr Junaid yace bai kamata mu bari wasu mutane su rinka jiya kasa ba alkalin Buhari muka zaba ba su ba. Yace mulki ana bayar wa ga wanda zai iya ba wai a dakko wanda bashi da cikakken lafiya da tsari a bashi ragamar babbar kasa kamar Nigeria ba.

Yace ba dole sai yan arewa za a ce za a zaba ba saidai duk wanda aka ga ya dave to a zabe shi dan ya kawo wa kasa cigaba.

An dade dai ana zargin shugaba Buhari da sakin ragamar kasa ga "cabals" wanda har me dakinshi Aisha Buhari ta taba yin maganar amma dai shi shugaba Buharin ya musanta zargin inda yace babu wani mataki da suka saka shi ya dauka ba tare da ra'ayinsa ba.

Shafin NAIJ.com Hausa ne ya koma LEGIT.ng Hausa

Latsa kuga sabuwar manhajar Legit.ng Hausa a wayarku ta salula: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Shafukanmu na dandalin sada zumunta sune:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel