Zabe: Yan sanda sun gargadi yan siyasa akan siyan kuri’u

Zabe: Yan sanda sun gargadi yan siyasa akan siyan kuri’u

- Hukumar yan sandan Najeriya ta gargadi yan siyasa da su guji siyan kuri’u a ranar zabe ko kuma su fuskanci doka

- Mataimakin sufeto janar na yan sanda da ke kula da hedkwatar rundunar yace siyan kuri’ a ranar zabe laifi ne sannan yan sanda ba za su yi kasa a gwiwa ba wajen kama duk wanda aka kama kan haka

- Ya bukaci yan siyasa da su yi siyasa cikin dattaku sannan su yi wasan daidai da doka

Rundunar yan sanda ta gargadi yan siyasa da su guji siyan kuri’u a ranar zabe ko kuma su fuskanci doka.

Mataimakin sufeto janar na yan sanda da ke kula da hedkwatar rundunar, Abuja, Usman Tilli, ya yi gargadi a Gombe a ranar Talata , 12 ga watan Janairu yayinda yake jawabi da masu ruwa da tsaki.

Zabe: Yan sanda sun gargadi yan siyasa akan siyan kuri’u

Zabe: Yan sanda sun gargadi yan siyasa akan siyan kuri’u
Source: UGC

Yace siyan kuri’ a ranar zabe laifi ne sannan yan sanda ba za su yi kasa a gwiwa ba wajen kama duk wanda aka kama kan haka.

“Kuna da damar siyan kuri’unku kafin zabe amma a ranar zabe ba a yarda da aka ba saboda laifi ne,” inji shi.

Mataimakin Shugaban yan sandan wanda ke da hakkin kula da zabe a yankin arewa maso gabas, yace yan sandan za ta bayar da sararin fafatawa ga dukkanin yan takarar siyasa.

Ya kuma bukaci yan siyasa da su yi siyasa cikin dattaku sannan su yi wasan daidai da doka.

KU KARANTA KUMA: Hotunan Zahra da Yusuf Buhari suna yiwa mahaifinsu kamfen a Abuja

A baya mun ji cewa mukaddashin shugaban rundunan yan sandan Najeriya, Mista Mohammed Adamu, yayi gargadi cewa babu dan sanda da zai yi tafiya tare da manyan mutane a ranar zabe.

Yace za a kama duk wani dan sanda da aka kama tare da manyan mutane a ranar zabe.

Haka zalika, ya bayyana cewa hukumomin tsaro zasu sanya idanu akan ma’aikatan wucin-gadi wadanda za a iya sauya ma ra’ayi, “musamman masu bautan kasa."

Sanarwa: Ku ci gaba da kasancewa tare da mu yayin da Shafin Naij.com Hausa ya sauya suna zuwa Legit.ng Hausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Domin shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.com

Ku biyo cikin shafukan mu na zaurukan sada zumunta:

https://facebook.com/legitnghausa

https://twitter.com/legitnghausa

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel