Don Allah ka da ku kori Ma’aikatan ku – Buhari ya roki ‘Yan kasuwa

Don Allah ka da ku kori Ma’aikatan ku – Buhari ya roki ‘Yan kasuwa

Mun ji labari daga jaridar Vanguard cewa shugaba Muhammadu Buhari yayi kira ga ‘yan kasuwa cewa su yi hakuri su guji sallamar ma’aikatan su a dalilin karin albashin da ake nema ayi a Najeriya kwanan nan.

Don Allah ka da ku kori Ma’aikatan ku – Buhari ya roki ‘Yan kasuwa

Shugaba Buhari ya yabawa Ngige kan karawa Ma'aikata albashi
Source: UGC

Kamar yadda mu ka ji, shugaban kasa Muhammadu Buhari ya fadawa ‘yan kasuwa ka da su kori kowa daga aiki a sakamakon maida karancin albashi zuwa akalla N30, 000 da za ayi. Buhari yayi wannan jawabi ne a Garin Legas.

A wata ganawa da shugaban kasar yayi da ‘yan kasuwan da ke cikin garin Legas, ya tabbatar masu da cewa gwamnatin sa za ta karawa ma’aikata albashi inda kowa zai rika tashi da abin da bai yi kasa da N30, 000 a kowane wata ba.

KU KARANTA: An raba wani mutumi da aikinsa saboda yana goyon bayan jam’iyyar adawa

Muhammadu Buhari ya yabawa babban ministan sa na kwadago watau Chris Ngige saboda irin namijin kokarin da yayi wajen ganin an karawa ma’aikatan kasar albashi inda ya rika fadi-tashi na tsawon watanni domin ganin an dace.

Buhari yayi zama ne da kungiyoyin ‘yan kasuwa dabam-dabam na kasar nan wadanda su ka hada da NECA, MAN, NACCIMA, da sauran su, inda a jawabin sa ya koka da cewa wasu jihohi ba su iya biyan albashi har sai da ya dafa masu.

Duk da halin da ake ciki dai, shugaban kasar yayi alkawarin karawa ma’aikata albashi yana kuma mai rokon ‘yan kasuwan masu zaman kan-su cewa ka da su kori ma’aikata saboda gudun nauyin albashi.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/legitnghausa

Ko a http://twitter.com/legitnghausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta LEGIT NG Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Shafin NAIJ Hausa ya koma LEGIT

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel