Hukuncin kotu: Gwamnatin Nigeria ba ta da ikon rufe asusun bankin Onnoghen

Hukuncin kotu: Gwamnatin Nigeria ba ta da ikon rufe asusun bankin Onnoghen

Wata babbar kotun gwamnatin tarayya ta haramtawa gwamnatin tarayya rufe asusun bankunan Walter Onnoghen, tsohon babban Alkalin Alkalai na kasa (CJN), har sai idan har kotu ce ta baiwa gwamnati umurnin yin hakan.

Onnoghen na fuskantar tuhuma a gaban kotun da'ar ma'aikata akan zarginsa da bayyana kadarorin bogi da kuma boye wasu makudan kudade na kasashen waje.

Mai shari'a Ijeoma Ojukwu ta bayar da wannan umurnin a ranar Litinin, bisa wata bukata da lauyan wanda ake kara ya gabatar mata, da kuma mataimakin shirin Ltd/GTE.

KARANTA WANNAN: Yanzunnan: EFCC za ta ci gaba da tsare Babachir Lawal bisa umurnin kotu

Hukuncin kotu: Gwamnatin Nigeria ba ta da ikon rufe asusun bankin Onnoghen

Hukuncin kotu: Gwamnatin Nigeria ba ta da ikon rufe asusun bankin Onnoghen
Source: Twitter

Mai shari'a Ojukwu ya ce: "Ya zama wajibi babban Antoni Janar na kasa ya samu umurni daga kotu kafin rufe asusun mai shari'a Onnoghen Walter."

An dage sauraron shari'ar har sai 13 ga watan Fabreru, 2019.

SANARWA: Shafin jaridar NAIJ.com Hausa ya sauya suna zuwa Legit.ng Hausa. Muna fatan za ka ci gaba da kasancewa tare da Legit.ng Hausa don karanta labarai da dumi duminsu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukan mu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel