Gaskiya an ci mutuncin Shugaban Kasa Buhari a Ogun – Tinubu

Gaskiya an ci mutuncin Shugaban Kasa Buhari a Ogun – Tinubu

- Asiwaju Bola Tinubu yace bai da niyyar barin APC sakamakon an jefe su jiya

- Tinubu yace Jam’iyyar PDP sun yi kokarin ruruta abin da ya faru kwanan nan

- Jigon na Jam’iyyar APC yayi tir da wulakancin da aka yi wa Shugaban kasar

Gaskiya an ci mutuncin Shugaban Kasa Buhari a Ogun – Tinubu

Bola Tinubu bai da niyyar ficewa daga Jam’iyyar APC
Source: Facebook

Mun ji labari cewa babban jigon jam’iyyar APC a Najeriya, Asiwaju Bola Ahmed Tinubu, yace bai da shirin barin jam’iyyar APC mai mulki a dalilin aturen da aka nemi ayi wa manyan jam’iyyar APC kwanan nan a cikin jihar Ogun.

Tsohon gwamnan na jihar Legas yayi maza yayi watsi da rade-radin cewa ya shirya barin APC a sakamakon abin da ya faru a jihar Ogun inda wasu ‘yan adawa su ka rika jifar su a lokacin da ake wani taron yakin neman zaben.

KU KARANTA: APC na fushi da gwamna Amosun saboda jifar Buhari da aka yi

Bola Tinubu yace yana nan a jam’iyyar APC har gobe inda yake bayani da yarbanci yace yana nan a APC “gidigba”, ma’ana dai babu gudu kuma babu ja da baya. Tinubu yayi wannan bayani ne ta wani hadimin sa watau Tunde Rahman.

Asiwaju Bola Tinubu ya kuma yi karin haske game da surutun da ake yi na cewa ya jefar da tutar jam’iyyar a wajen taron APC. Tinubu yace ya mikawa Adams Oshiomhole tutar ne da nufin a mikawa ‘dan takarar Gwamnan na su.

Mista Tunde Rahman wanda yake magana a madadin jagoran na APC yace ‘yan adawa su na ririta labarin fiye da yadda ya kamata inda yace abin da aka yi na jifan manya wajen gangamin na APC cin mutunci ne ga shugaban kasa Buhari.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/legitnghausa

Ko a http://twitter.com/legitnghausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta LEGIT NG Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Shafin NAIJ Hausa ya koma LEGIT

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel