Hotunan Zahra da Yusuf Buhari suna yiwa mahaifinsu kamfen a Abuja

Hotunan Zahra da Yusuf Buhari suna yiwa mahaifinsu kamfen a Abuja

An gano Zahra da Yusuf Buhari, yayan Shugaban kasa mai ci, yayinda suke yiwa mahaifinsu da abokin takararsa Osinbajo kamfen a Abuja.

Yan uwan junan da suka zama shahararru tun bayan da mahaifinsu ya kama aiki a 2015 na kokarin guje ma idanun duniya inda suke killace kansu daga taron jama’a.

Ku tuna Zahra wacce ke auran dan biloniya, Ahmed Indimi ta haifi danta kwanakin baya amma sun ki bayyana cikakke bayani da hoton yaron a kafafen sadarwa.

A bangaren Yusuf yan Najeriya da dama sun shiga damuwa lokacin da yayi hatsarin babur a shekarar 2017.

Sai dai a yanzu da zabe ya kuma ahlin Shugaban kasar sun zabi shiga sahun sauran yan Najeriya dn yiwa mahaifinsu kamfen duk da rade-radin cewa iyalan na guje ma kamfen.

KU KARANTA KUMA: Zabe: Za a kama duk dan sandan da aka gani tare da wani babba - IGP Adamu

Wadannan hotunan ya tabbatar da cewar Zahra da dan uwanta Yusuf na goyon bayan mahaifinsu da mataimakinsa, Osinbajo a zaben ranar 16 ga watan Fabrairu.

An gano su biyun sanye da rigar APC, wula da kuma madubi mai rage hasken rasa yayinda suke shiga unguwannin Abuja don goyon bayan tazarcen Buhari/Osinbajo.

Kalli hotunan a kasa:

Hotunan Zahra da Yusuf Buari suna yiwa mahaifinsu kamfen a Abuja

Hotunan Zahra da Yusuf Buari suna yiwa mahaifinsu kamfen a Abuja
Source: UGC

Hotunan Zahra da Yusuf Buari suna yiwa mahaifinsu kamfen a Abuja

Hotunan Zahra da Yusuf Buari suna yiwa mahaifinsu kamfen a Abuja
Source: UGC

Sanarwa: Ku ci gaba da kasancewa tare da mu yayin da Shafin Naij.com Hausa ya sauya suna zuwa Legit.ng Hausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Domin shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.com

Ku biyo cikin shafukan mu na zaurukan sada zumunta:

https://facebook.com/legitnghausa

https://twitter.com/legitnghausa

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel