An raba wani ma’aikacin gwamnati da aikinsa a Kaduna saboda goyon bayan jam’iyyar PDP

An raba wani ma’aikacin gwamnati da aikinsa a Kaduna saboda goyon bayan jam’iyyar PDP

Wani ma’aikacin gwamnati, Bala Gimba dake aiki a hukumar kiwon lafiya a matakin farko na karamar hukumar Soba ya yi ta aikinsa, inda hukumar ta sallameshi daga aiki har abada saboda yana goyon bayan jam’iyyar adawa, jam’iyyar PDP.

Mataimakin daraktan hukumar, Mohammed Murtala ne ya rattafa hannu akan takardar sallamar da hukumar ta aika ma Gimba, a karkashin umarnin shugaban karamar hukumar, Mohammed Makama, kamar yadda jaridar Daily Nigerian ta ruwaito.

KU KARANTA: 2019: El-Rufai ya bayyana manyan dalilai guda 4 kwarara da zasu kayar da Atiku

Majiyar Legit.ng ta ruwaito wasikar da hukumar ta aika ma Gimba na kunshe da laifukan da take zarginsa da aikatawa, inda ta zargeshi da shiga cikin harkokin siyasa tsundum duk da cewa yana ma’aikacin gwamnati, wanda yin hakan karya dokar aikin gwamnati ne.

“Duba da laifukan da Bala Abdu Gimba ya tafka ta hanyar shigarsa siyasa wanda hakan ya saba ma dokokin aikin gwamnati, da kuma tattara magoya bayansa tare da basu umarnin jifan gwamnan jahar Kaduna Nasir El-Rufai da shugaban karamar hukumar Soba yayin da suka kai ziyarar yakin neman zabe.

“Haka zalika da laifin furta muggan kalamai akan gwamnan da kuma tayar da hankali a yayin yakin neman zabennasa, an dakatar da shi daga aiki, dakatarwa ta dindindin daga ranar 30 ga watan Janairu, kuma n tsayar da albashinsa.” Inji wasikar.

Sai dai da Malam Abdu Gimba ya musanta laifukan da karamar hukumar ke zarginsa da aikatawa, inda yace bai taba tattara magoya bayan PDP su jefi gwamna ko cin mutuncinsa , asalima babu wani jifa da aka yi, sai dai shine ma wanda ya taushi yayan jam’iyyar APC da basa shiri da gwamnan yayin ziyarar daya kai mazabar Gimba.

Amma dangane da kasancewarsa dan jam’iyyar PDP kuwa, Gimba yace; “Tunda kowanne dan Najeriya yana da yancin goyon bayan jam’iyyar siyasa, don haka na kasance dan PDP, kuma inada wannan yancin. Babbar matsalar itace mazabarmu daya da Ciyaman, kuma ya san na fi shi jama’a anan shi yasa yayi min haka.”

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Source: Legit

Mailfire view pixel