Mataimakin Shugaban kasa Osinbajo ya fadawa mutanen Ogun su yi APC sak

Mataimakin Shugaban kasa Osinbajo ya fadawa mutanen Ogun su yi APC sak

Mun samu labari cewa mataimakin shugaban kasa Farfesa Yemi Osinbajo yayi kira ga mutanen jihar Ogun su zabi jam’iyyar APC mai mulki tun daga sama har kasa a zabe mai zuwa da za ayi kwanan nan.

Mataimakin Shugaban kasa Osinbajo ya fadawa mutanen Ogun su yi APC sak

Osinbajo ya caccaki Gwamna Amosun na juyawa APC baya
Source: Depositphotos

Farfesa Yemi Osinbajo, ya nemi mutanen jihar Ogun su yi watsi da kiran da gwamnan su Ibikunle Amosun yake yi na cewa jama’a su kauracewa duk wani ‘dan takarar jam’iyyar APC face shugaban kasa Muhammadu Buhari.

Mai girma Yemi Osinbajo ya fadawa mutane su zabi duk ‘dan takarar da APC ta tsaida a zaben na 2019. Haka kuma mataimakin shugaban kasar yayi shagube yana sukar wadanda ke kira a zabi ‘yan takarar wasu jam’iyyu dabam.

KU KARANTA: Gwamnan Jihar Ogun yayi magana a kan marawa Buhari baya

Osinbajo yayi wannan jawabi ne da yaren yarbanci a lokacin da ya zauna da mutanen Yankin Ijebu da ke cikin Garin na Ogun jiya. An yi wannan zama ne a fadar Mai Martaba Sarki Ebunmawe Ago Iwoye watau Abdulrazak Adenugba.

A cewar mataimakin shugaban kasar, duk wadanda su ke cikin jam’iyyar APC kuma su ke kiran a zabi wasu ‘yan takara dabam, su ne bara-gurbin da ke cikin jam’iyyar. Osinbajo ya kara jawo hankalin jama’a da cewa su zabi duk 'Yan APC.

Matimakin na shugaba Buhari ya sake bayyana wannan a lokacin da ya gana da wasu ‘yan kasuwa a Ijebu Ode da ke cikin jihar Osun. Osinbajo yace Buhari ba barawo bane kuma gwamnatin sa ta tanadi hanyoyin taimakawa Talakan kasar.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/legitnghausa

Ko a http://twitter.com/legitnghausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta LEGIT NG Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Shafin NAIJ Hausa ya koma LEGIT

Source: Legit

Mailfire view pixel