Kuma dai: Jam’iyyar PDP ta sake maka Buhari gaban kotu akan zaben 2019

Kuma dai: Jam’iyyar PDP ta sake maka Buhari gaban kotu akan zaben 2019

Rikicin siyasar Najeriya baya taba karewa, musamman a yanzu da babban zaben 2019 ya rage saura kwanaki biyu kacal, domin kuwa a yanzu haka jam’iyyar PDP ta shigar da karar shugaban kasa Muhammadu Buhari gaban kotu.

PDP ta shigar da Buhari kotun ne bisa halartar wasu gwamnonin kasar Nijar guda biyu zuwa wajen gangamin yakin neman zabensa daya gudana a jahar Kano, a ranar 31 ga watan Janairu, gwamnonin sun hada da gwamnan Zinder Issa Moussa da gwamnan Maradi, Zakiri Umar.

KU KARANTA:Miyagun yan bindiga sun yi garkuwa da wasu Mata guda 2 a Kaduna

Kuma dai: Jam’iyyar PDP ta sake maka Buhari gaban kotu akan zaben 2019

Ganduje tare da gwamnonin Nijar
Source: UGC

Majiyar Legit.ng ta ruwaito PDP ta shigar da Buhari kara ne a gaban babbar kotun tarayya dake babban birnin tarayya Abuja, inda ta nemi kotun ta yi mata karin haske game da halartar gwamnonin zuwa taron, domin gane ko hakan ya saba ma dokokin Najeriya.

A cewar PDP, sashi na 12 na kundin dokokin Najeriya na shekarar 2010 ya bayyana cewa yan Najeriya ne kadai zasu iya shiga duk wani harkar zabe a kasar, don haka PDP ta nemi kotun tayi gaggawar yanke hukunci a shari’ar kafin zabe, saboda a cewarta rikicin kafin zabe ne wannan.

“Abinda muke nema daga kotu shine ta yanke hukunci cewa duba da sashi na 12, duk wasu bakin haure ko kuma wadanda bay an Najeriya ba, basu da hurumin shiga ko wacce irin harka da ta shafi zabe a Najeriya.

“Muna neman kotu ta yanke hukuncin cewa halartar gwamnoni kasar Nijar guda biyu gangamin yakin neman zaben Buhari ya saba ma dokokin Najeriya.” Inji lauyan jam’iyyar PDP Adedamola Fanokun.

Sauran wadanda PDP ta hada cikin karar da ta shigar da Buhari sun hada da hukumar zabe mai zaman kanta, INEC, hukumar kula da shige da fice ta kasa, Ministan al’amuran cikin gida Abdulrahman Dambazau da kuma uwar jam’iyyar APC.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel