Siyasar Kano: Wasu ‘Yan daba sun shiga gidan dangin Abba Yusuf

Siyasar Kano: Wasu ‘Yan daba sun shiga gidan dangin Abba Yusuf

Mun samu labari cewa wasu ‘yan daba sun kai hari gidan Injiniya Abba Kabiru Yusuf wanda shi ne ‘dan takarar gwamna na jam’iyyar PDP mai adawa a jihar Kano a cikin daren Talatar jiya.

Siyasar Kano: Wasu ‘Yan daba sun shiga gidan dangin Abba Yusuf

Kwanan nan aka kona gidan Injiniya Abba Yusuf a Kano
Source: Facebook

Kamar yadda labari ya iso mana ta bakin kwamitin yakin neman zaben ‘dan takarar, wadannan ‘yan daba sun shiga gidan dangin Abba Kabiru Yusuf ne da kuma na wani hadimin sa mai suna Mustapha Ibrahim Chigari.

Wannan mummunan abu ya faru ne a cikin tsakar daren Ranar Talata da kimanin karfe 1:00 inji kakakin yakin neman zaben Abba K. Yusuf. An yi dace dai ba a rasa rai ko guda wajen wannan mummunan hari da aka kai ba.

KU KARANTA: An kone ofishin kamfen din dan takarar gwamna a PDP

Har da Makwabtan Injiniya Abba Yusuf sai da aka kutsa cikin gidajen su da ke cikin Chiranci a karamar hukumar Gwale da ke cikin Birnin. An dai yi kokarin samun jami’an tsaro a yankin amma abin ya ci tura a lokacin.

PDP tana zargin cewa wasu na kusa da shugaban jam’iyyar APC warau Abdullahi Abbas ne ya sa aka kitsa wannan danyen aiki ta hannun wasu manyan ‘yan daba 2 da su kayi fice a jihar Kano wajen tada rikici.

Sanusi Bature Dawakin Tofa wanda shi ne ke magana da yawun bakin ‘dan takarar jam’iyyar PDP na jihar Kano a zaben na 2019 watau Injiniya Abba Kabiru Yusuf ne ya fitar da wannan jawabi a jiya.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/legitnghausa

Ko a http://twitter.com/legitnghausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta LEGIT NG Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Shafin NAIJ Hausa ya koma LEGIT

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel