Daga karshe, jam'iyyar APC ta fadi abunda zata yi wa wadanda suka jefi shugaba Buhari a Ogun

Daga karshe, jam'iyyar APC ta fadi abunda zata yi wa wadanda suka jefi shugaba Buhari a Ogun

Jam'iyyar mai mulki a tarayyar Najeriya ta All Progressives Congress (APC) ta bayyana takaicinta kan yadda aka jefi shugabanninta da suka hada da shugaba Muhammadu Buhari a gangamin yakin neman zaben shugaba Buhari a jihar Ogun.

Wannan dai na kunshe ne a cikin wata sanarwar manema labarai da jam'iyyar ta APC ta fitar inda ta ce za ta dauki tsattsauran mataki kan gwamnan jihar Ibikunle Amosun wanda ta zarga da shirya cin mutuncin ga Buhari da kuma shugabanta Adams Oshiomhole.

Daga karshe, jam'iyyar APC ta fadi abunda zata yi wa wadanda suka jefi shugaba Buhari a Ogun

Daga karshe, jam'iyyar APC ta fadi abunda zata yi wa wadanda suka jefi shugaba Buhari a Ogun
Source: Twitter

KU KARANTA: Kafin karfe 12 na ranar Asabar Buhari ya sha kasa - Adam Zango

Legit.ng Hausa ta samu dai cewa a ranar Litinin ne wasu suka jefi Adams Oshiomhole a yayin da shugaba Muhammadu Buhari ke gangamin zabensa a birnin Abeokuta.

An jefi Oshiomhole ne bayan da ya ambaci sunan dan takarar gwamna na APC a jihar, Mista Dapo Abiodun wanda gwamnan jihar ba ya goyon baya, matakin da ya harzuka mutanen da suka halarci gangamin.

APC ta ce ba za ta lamunce wa wannan rashin da'a ba daga duk wani mambanta. Ta ce za ta yi nazari kan abin da ya faru inda aka kunyata Buhari da shugabanninta kuma za ta dauki mataki akai bayan an kammala zabe.

Lamarin ya kai sai da jam'ian tsaro suka rika kare shugaba Buharir daga masu jifa kafin kammala taron.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma legit.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://web.facebook.com/legitnghausa?_rdc=1&_rdr

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.com

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel