Mutuwar magoya bayan jam'iyyar APC: Buhari ya mika sakon ta'aziyya

Mutuwar magoya bayan jam'iyyar APC: Buhari ya mika sakon ta'aziyya

Shugaba Muhammadu Buhari ya bayyana bakin cikinsa game da rasuwar wasu daga cikin magoya bayan jam'iyyar All Progressives Congress (APC) da suka rasu sakamakon cinkoso a wurin kaddamar da yakin neman zaben shugaban kasa da akayi a Fatakwal na jihar Rivers a ranar Talata.

Sanarwar da ta fito daga mataimakin shugaban kasa na musamman a fanin watsa labarai, Garba Shehu ta ce Shugaban kasa Buhari ya yi matukar bakin ciki dangane da rasa rayyukan da akayi kuma ya mika sakon ta'aziyyarsa ga yan uwa da abokan wadanda suka rasu.

Ya kuma yi addu'an samun sauki cikin gaggawa ga wadanda suka jikkata.

DUBA WANNAN: Dalilin da yasa al'ummar Adamawa za su zabi Buhari - Talban Adamawa

Mutuwar magoya bayan jam'iyyar APC: Buhari ya mika sakon ta'aziyya

Mutuwar magoya bayan jam'iyyar APC: Buhari ya mika sakon ta'aziyya
Source: Twitter

Shugaban kasan ya ce "rashin tsara hanyoyin da mutane za su fice daga filin wasa na Adokiye Amiesmaka Stadium ne ya janyo rasa rayyukan wadda hakan yasa aka tashi a taron cikin bakin ciki.

"Abin bakin ciki ne yadda mutanen da suke da rawar da za su taka wurin gina kasar mu a nan gaba da suka zo su saurari yadda gwamnatinsu ke kokarin kawo cigaba a kasar su suka rasu a wurin taron.

"Ina tabbatarwa al'umma cewa jam'iyyar mu da gwamnati za tayi duk mai yiwa domin kiyaye lafiya duk mutanen da za su hallarci taron kaddamar da yakin neman zabe da wasu tarukkan siyasa," inji shugaban kasar.

Shugaban kasar ya ce gwamnatin tarayya za ta saka wadandu suka rasu cikin addu'a tare da bayar da tallafi ga iyalensu a wannan mawuyacin halin da suke ciki.

Ya yi addua'a Allah ya gafartawa wadanda suka rasu.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: : https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel