Gwamnan Jihar Bauchi ya yi rashin wani dan uwan sa na jini

Gwamnan Jihar Bauchi ya yi rashin wani dan uwan sa na jini

Da sanadin shafin jaridar Daily Trust mun samu rahoton cewa, gwamnan jihar Bauchi, Muhammad Abdullahi Abubakar, ya yi babban rashin na wani dan uwan sa na jini da ya kasance tamkar kani ko kuma yaya a gare sa.

Sakataren yada labarai na fadar gwamnatin jihar, Abubakar El-Sadique, shine ya bayar da tabbacin hakn cikin wata sanarwa a yau Talata yayin ganawa da manema labarai cikin birnin na Bauchin Yakubu.

Gwamnan Jihar Bauchi; Muhammad Abdullahi Abubakar

Gwamnan Jihar Bauchi; Muhammad Abdullahi Abubakar
Source: Depositphotos

Majiyar jaridar Legit.ng ta ruwaito cewa, Abubakar Hassan Abubakar, wanda ake yiwa lakabi da Yaya Bala, dan uwa shakiki ga Gwamna Abubakar ya riga mu gidan gaskiya a yau Talata cikin birnin Jos da ke jihar Filato.

El-Sadique cikin jawaban sa ya ce Marigayi Yaya Bala ya riga mu gidan gaskiya bayan ya sha fama da wata 'yar takaitacciyar rashin lafiya da ta yi sanadiyar ajalinsa. Ya ce ya rasu ya bar 'ya'ya 14 tare da jikoki kimanin sittin a duniya.

KARANTA KUMA: Mai gida na mutum ne mai tausayi da ƙaunar al'umma - Aisha Buhari

Jaridar Legit.ng ta ruwaito cewa, an gudanar da jana'izar Marigayi Yaya Bala cikin birnin Jos idan aka sanya a makwanci bisa tanadi da kuma tafarki irin na addinin Islama.

A yayin haka jaridar ta kuma ruwaito cewa, wakilin shiyyar Kaduna ta Tsakiya a zauren majalisar dattawan Najeriya, Sanata Shehu Sani, yayi ikirarin cewa 'yan ta'adda sun salwantar da rayukan Mutane 21 cikin garin Birnin Gwari a tsakanin ranakun Alhamis da kuma Juma'a na makon da ya shude.

Sanarwa: Ku ci gaba da kasancewa tare da mu yayin da Shafin Naij.com Hausa ya sauya suna zuwa Legit.ng Hausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Domin shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.com

Ku biyo cikin shafukan mu na zaurukan sada zumunta:

https://facebook.com/legitnghausa

https://twitter.com/legitnghausa

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel