'Yan daba sun lalata motar yakin neman zaben APC a Kano

'Yan daba sun lalata motar yakin neman zaben APC a Kano

Salihu Tanko Yakasai, mai taimakawa gwamnan jihar Kano a bangaren sadarwar zamani, ya zargi wasu ‘yan daba da ke goyon bayan tafiyar Kwnkwasiyya da lalata motar yakin neman zaben jam’iyyar APC a kan titin zuwa Katsina da ke birnin Kano.

Yakasai ya ce ‘yan dabar da ke dauke da muggan makamai sun far wa motar yakin neman zaben APC da sara da duka a yayin da tawagar magoya bayan Kwankwasiyya ke wuce wa ta titin zuwa Katsina.

Kazalika, ya zargi ‘yan dabar da ya ce na Kwankwasiyya ne da kai farmaki shagunan ‘yan kasuwa da ke kan titin Inrahim Taiwo da Beirut.

DUBA WANNAN: Asarar kujeru 50 a APC: Buhari ya bayyana rashin jin dadin sa

'Yan daba sun lalata motar yakin neman zaben APC a Kano

'Yan daba sun lalata motar yakin neman zaben APC a Kano
Source: Twitter

'Yan daba sun lalata motar yakin neman zaben APC a Kano

'Yan daba sun lalata motar yakin neman zaben APC a Kano
Source: Twitter

Adawar siyasa tsakanin bangaren gwamna Ganduje na jam’iyyar APC da tsagin Kwankwasiyya na jam’iyyar PDP na daukan sabon salo a jihar Kano.

Ko a yau, Talata, sai da sarkin Kano, Muhammadu Sanusi II, ya gargadi ‘yan siyasa da su guji jefa jihar Kano cikin rikicin siyasa.

'Yan daba sun lalata motar yakin neman zaben APC a Kano

'Yan daba sun lalata motar yakin neman zaben APC a Kano
Source: Twitter

'Yan daba sun lalata motar yakin neman zaben APC a Kano

'Yan daba sun lalata motar yakin neman zaben APC a Kano
Source: Twitter

Ko a jiya, Talata, sai da Legit.ng ta wallafa rahoton cewar sabon kwamishinan rundunar ‘yan sanda a jihar Kano, Mista Moohammed Wakili, ya ce jami’an rundunar ‘yan sanda sun kama wasu batagari 28 bisa alakar da su ke da ita a harin da aka kai gidan shugaban jam’iyyar APC a jihar Kano, Abdullahi Abbas, yayin taron yakin neman zaben dan takarar shugaban kasa a jam’iyyar PDP da aka yi ranar Lahadi a Kano.

Da ya ke jawabi ga manema labarai a hedikwatar rundunar ‘yan sanda ta Kano da ke unguwar Bompai, Wakili ya ce an fara gudanar da bincike a kan lamarin tare da bayyana cewar rundunar ‘yan sanda za ta dauki mataki a kan duk wanda ke da hannu a kan afkuwar lamarin, duk girma ko matsayin sa.

Wakili ya bayyana cewar a shirye ya ke domin daukan matakin da zai samar da zaman lafiya a jihar Kano kafin da kuma bayan kamala zabe. Kazalika ya yi kira ga ‘yan siyasa da su kasance ma su girmama doka tare da bayar da tabbacin cewar rundunar ‘yan sanda za ta kasance mai adalci ga kowa da kowa.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel