Zaben 2019: Gwamnati ta bankado sabuwar hanyar da Atiku ya shirya tafka gagarumin magudi

Zaben 2019: Gwamnati ta bankado sabuwar hanyar da Atiku ya shirya tafka gagarumin magudi

Gwamnatin tarayyar Najeriya ta ce jam'iyyar adawa ta PDP tare da dan takarar ta na shugaban kasa da sauran jiga-jigan ta sun dauri aniyar haifar da rikici da tarzoma da za ta kawo yamutsi har ta kai ga lalata zabukan gama gari da ake shirin yi.

Ministan yada labarai na gwamnatin tarayyar, Mista Lai Mohammed ne dai ya bayyana hakan a wani taron manema labarai da ya gudanar a ofishin sa dake a garin Abuja, babban birnin tarayyar Najeriya.

Zaben 2019: Gwamnati ta bankado sabuwar hanyar da Atiku ya shirya tafka gagarumin magudi

Zaben 2019: Gwamnati ta bankado sabuwar hanyar da Atiku ya shirya tafka gagarumin magudi
Source: Twitter

KU KARANTA: An kama mutane 50 da laifin fada lokacin zuwan Atiku Kano

Legit.ng Hausa ta samu cewa Lai Mohammed ya bayyana cewa suna da labarin kiran taron manema labarai da jam'iyyar ta PDP ta shirya a wani mataki na farfaganda domin ta jefa tsoro a cikin zukatan al'ummar kasa dama kasashen duniya game da zaben.

Ya kara da cewa jam'iyyar ta PDP kamar yadda suka samu rahotannin sirri, tana shirin yiwa gwamnatin tarayya da kuma hukumar zaben kazafi sannan kuma ta bata masu suna a idon duniya duk don dai aga kamar ba sahihin zabe aka gudanar ba.

A baya ma dai, Kungiyar nan dake goyon bayan tazarcen Shugaba Muhammadu Buhari a zabukan 2019 da tafi maida hankali musamman a fannin yada labarai watau Buhari Media Organisation (BMO) a turance ta bankado wani sabon salon magudi da suka ce Atiku da PDP sun shirya yi.

A cikin wata sanarwar manema labarai da shugabanta da kuma Sakataren kungiyar suka fitar, sun bayyana cewa jam'iyyar ta adawa da dan takarar ta sun ware makudan kudade domin daukar nauyin magoya bayan su don ganin sun samu shiga cikin ma'aikatan zaben da za'a yi.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma legit.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://web.facebook.com/legitnghausa?_rdc=1&_rdr

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.com

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel