Mai gida na mutum ne mai tausayi da ƙaunar al'umma - Aisha Buhari

Mai gida na mutum ne mai tausayi da ƙaunar al'umma - Aisha Buhari

Uwar gidan shugaban kasa Muhammadu Buhari, Aisha, a yau Talata tayi karin haske dangane wasu dabi'un Mai gidan ta sabanin yadda wasu ke jingina ma sa dabi'u na tsanani da rashin jin kai ko kuma hali na ko in kula.

A yayin da ake daf da gudanar da babban zaben kujerar shugaban kasa, Aisha a yau Talata ta ce mai gidan ta da ya kasance shugaban kasar Najeriya mutum ne mai tsananin tausayi gami jin kai da nuna ga ƙauna ga al'umma.

Aisha wadda ta jagoranci tawagar Mata da Matasa na kungiyar yakin neman zaben Buhari, ta bayyana hakan ne a hedikwatar cibiyar ma'aikatan sufurin ta NURTW da ke babban birnin kasar nan na tarayya.

Mai gida na mutum ne mai tausayi da ƙaunar al'umma - Aisha Buhari

Mai gida na mutum ne mai tausayi da ƙaunar al'umma - Aisha Buhari
Source: Depositphotos

Kamar yadda shafin jaridar Vanguard ya ruwaito, Uwargidan shugaban kasar ta jagoranci tawagar kungiyar yakin neman zaben Buhari zuwa cibiyar ma'aikatan na Sufuri domin labarta ma su yadda jagoranci na gwamnatin Buhari za ta yi tasiri wajen inganta jin dadin su na rayuwa.

Rahotanni sun bayyana cewa, jagoran kungiyar Mata da Matasa ta yakin neman zaben Buhari, Birgediya Janar Buba Marwa mai ritaya, shine ya wakilcin uwargidan shugaban kasar yayin wannan babban taro na neman magoya baya.

KARANTA KUMA: Cikin Hotuna: Taron yakin zaben Atiku a jihar Legas

Uwar gidan shugaban kasar ta ce gwamnatin Buhari ta yi kwazon gaske tsawon shekaru kimanin hudu da ta shafe a bisa karagar mulki inda ta ce tsantsar gaskiyar sa ce ta yi tasiri wajen nasarorin da kasar nan ta samu ta fuskar ci gaba.

Cikin wani rahoton mai nasaba da wannan, a yau Talata shugaban kasa Buhari ya gudanar da taron sa na yakin neman zabe cikin jihar Ribas da kuma Bayelsa yayin da dan takarar kujerar shugaban kasa na jam'iyyar PDP, Atiku Abubakar ya gudanar da na sa taron cikin jihar Legas.

Sanarwa: Ku ci gaba da kasancewa tare da mu yayin da Shafin Naij.com Hausa ya sauya suna zuwa Legit.ng Hausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Domin shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.com

Ku biyo cikin shafukan mu na zaurukan sada zumunta:

https://facebook.com/legitnghausa

https://twitter.com/legitnghausa

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel