Yanzun nan: Rundunar sojin Najeriya na batakashi da yan Boko Haram a Madagali

Yanzun nan: Rundunar sojin Najeriya na batakashi da yan Boko Haram a Madagali

Rahotanni daga garin Madagali, arewacin jihar Adamawa na nuna cewa ana batakashi tsakanin yan kungiyar Boko Haram da dakarun sojin Najeriya da yammacin Talata, 12 ga watan Febrairu, 2019.

Hukumar sojin Najeriya ta bayyana cewa bayan wannan artabu, sun hallaka yan Boko Haram da dama.

Mataimakin diraktan yada labaran hukumar soji, Kanal Ado Isa, ya saki jawabin cewa jami'an sojin 143 Bataliya sun ragargaji yan Boko Haramun yayinda sukayi kokarin kai hari barikin sojoji.

Yace: "Jami'an sojin 143 Battalion, 28 Task Force Brigade, Sector 1 na Operation Lafiya Dole da aka tura Madagali, jihar Adamawa sun samu nasarar ragargazan yan ta'addan Boko Haram ranan Asabar da sukayi kokarin shiga barikin Soji misalin karfe 6 na yamma."

"Yan ta'addan sun shigo da motoci kuma sun gamu da ajalinsu daga hannun dakarun soji. Sojin sun hallakasu kuma sun lalata makamansu."

"A yayin batakashin, sojin sun kashe yan Boko Haram da dama, sun damke daya da rai yayinda wasu sun arce da raunuka."

"Sojin sun kwato bindigan AK47 biyar, carbin harsasai hudu, girnet 1.. Sun kwato wayoyi biyu da na'urar daukan hoto kirar Sony. Abin takaici, jami'in soja daya da wani mutum sun rasa rayukansu kuma mutane biyar sun jikkata amma suna asibiti"

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel