Zabe: Za a kama duk dan sandan da aka gani tare da wani babba - IGP Adamu

Zabe: Za a kama duk dan sandan da aka gani tare da wani babba - IGP Adamu

- IGP Mohammed Adamu, yayi gargadi cewa babu dan sanda da zai yi tafiya tare da manyan mutane a ranar zabe

- Yace za a kama duk wani dan sanda da aka kama tare da manyan mutane a ranar zabe

- Adamu Haka ya kuma ce hukumomin tsaro zasu sanya idanu akan ma’aikatan wucin-gadi wadanda za a iya sauya ma ra’ayi

Mukaddashin shugaban rundunan yan sandan Najeriya, Mista Mohammed Adamu, yayi gargadi cewa babu dan sanda da zai yi tafiya tare da manyan mutane a ranar zabe.

Yace za a kama duk wani dan sanda da aka kama tare da manyan mutane a ranar zabe.

Zabe: Za a kama duk dan sandan da aka gani tare da wani babba - IGP Adamu

Zabe: Za a kama duk dan sandan da aka gani tare da wani babba - IGP Adamu
Source: UGC

Adamu, ya yi gargadin ne yayinda yake magana a taron gabatar da hadin gwiwa tsakanin kungiyoyin Transition Monitoring Group, the Human and Environmental Development Agenda, hukumar yan sanda, hukumar yaki da cin hanci da rashawa mai zaman kanta da sauran hukumomi da ke hukunta masu laifi.

Haka zalika, ya bayyana cewa hukumomin tsaro zasu sanya idanu akan ma’aikatan wucin-gadi wadanda za a iya sauya ma ra’ayi, “musamman masu bautan kasa."

KU KARANTA KUMA: Zolaya Buhari ke yi cewa da yayi kowa ya cika cikin sa in ma fitinan ne aje ayi – Kwamitin Kamfen

”Mista Adamu ya baiwa yan Najeriya tabbacin samar da tsaro a ranakun zabe.

Mukaddashin shugaban rundunan yan sandan ya kuma koka inda ya bayyana cewa: “Muna da labarin ana shigowa da Kayan yan sanda na bogi cikin kasar.”

Sanarwa: Ku ci gaba da kasancewa tare da mu yayin da Shafin Naij.com Hausa ya sauya suna zuwa Legit.ng Hausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Domin shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.com

Ku biyo cikin shafukan mu na zaurukan sada zumunta:

https://facebook.com/legitnghausa

https://twitter.com/legitnghausa

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel